Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya amince da soke bashin da gwamnati take bin kamfanin NNPC bilyan biyar da dori, Kamar yadda fadar shugaban kasa ta fada ranar Litinin.
Wannan mataki yana daga cikin shirin da shugaba Tinubu ya dauka domin sabunta asusun NNPC da zummar bayyana komi gameda kamfanin a dai dai lokacin da NNPC yake fuskanar karancin kudade, da kuma dumbin bashi dake kansa, gabannin shirin gwamnati ta sayar da hannayen jari a bangaren mai da iskar gas.
Basussukan kamfanin NNPC da gwamnati ta soke abunda ya kama har zuwa 31 ga shekarar da ta wuce ne.
Amma basussukan da ake bin kamafani NNPC daga watan Janairu zuwa oktoban bana har yanzu wannan bashi yana kansa.
Fadar shugaban kasan ta ci gaba da cewa har yanzu ana gardama kan kudade fiyeda dala biyan 42 da ya kamata ace NNPC ya mikawa gwamnati tsakanin shekara ta 2011-2017, NNPC dai ta dage cewa ta baiwa gwamnati dukkan kudade da ya kamata ta mika mata.
Burin gwamnati da daukar wannan mataki shine kara bayyana ayyukan kamfanin domin kawar da duk wani zato ko kumbiya kumbiya, da kuma kawo daidaito tsakanin kamfanin da kuma gwamnati wacce ta dogara sosai kan kudaden shiga ta fuskar mai.


