Shugaban ‘yan hamayya a Uganda Bobi Wine ya fada cewa, an kai matarsa asibiti, sakamakon farmaki da sojoji suka kai gidansa suka shake matar, kusan suka tsiraice ta.
Bobbi Wine mawakin zamani da ya rikida ya zama dan siyasa, ba ya gidan, tun bayan da ya tsere daga wani farmakin farko da jami’an tsaron suka kai gidansa, jim kadan kamin hukumomin zaben kasar suka ayyana shi a zaman wanda ya zo na biyu a zaben da aka yi ranar 15 ga watan nan na Janairu. Bobi Wine dai yanzu yana boye.
A cikin dare, sojoji da karfin tsiya suka balla kofofi suka shiga gidansa dake Kampala, suka doki ma’aikata, kamar yadda Bobi Wine ya fada a sakon da ya wallafa a shafinsa a dandalin X.
Babban hafsan sojojin Uganda Muhoozi Kainerugaba, wanda kuma dan shugaba Yuweri Museveni ne, ya fada ranar jumma’a cewa, hukumomin kasar sun kashe magoyan bayan jam’iyyar Bobi Wine NUP 30, kuma ta tsare magoya bayan jam’iyyar dubu 2. Hukumomi dai basu tuhumi Bobi Wine da wani laifi ba.
Duk kokarin jin ta bakin kakakin sojojin Uganda Chris Magezi bai yi nasara ba.
A ranar Alhamis dai babban Sakataren MDD Antonio Gutierrez, ya bayyana damuwa kan kamen da kuma tarzoma da take shafar ‘yan hamayya.


