Wani gungun hafsoshin soja a kasar Guinea-Bissau sun ce sun kwace mulki jiya Laraba, kwana guda kafin hukumar zaben kasar ta bada sakamakon zaben shugaban kasar da aka yi cikin wannan mako.
A cikin wata sanarwar da kakakinsu Diniz N’Tchama ya karanta a Telebijin na kasa, sojojin sun ce sun kawar da shugaba Umaro Sissoco Embalo daga kan mulki, sun dakatar da aikin zabe na kasar, suka rufe bakin iyakoki kuma sun kafa dokar hana fita cikin dare.
Jim kadan a bayan wannan, Embalo ya fada ma gidan telebijin na France24 cewa an cire shi daga kan kujerarsa.
Sojojin suka ce sun kafa majalisar mulki ta maido da oda a kasar, kuma sune zasu ci gaba da mulkin kasar har sai illa ma sha Allahu.
Sojojin ba su ce ko sun kama shugaba Embalo ba, ammam wasu majiyouyin tsaro biyu a kasar sun shaidawa kamfanin dillanin labarai na Reuters cewa ana tsare da shi a ofishin babban hafsan sojojin kasar.
A cikin wani bidiyon da ofishin kyamfe nasa ya rarraba cikin daren Larabar nan, babban mai kalubalantar Embalo a zaben, Fernando Dias, yace yana nan boye a wani wuri a bayan da wasu mutane dauke da makamai suka yi kokarin kama shi.
Dias yace an kama tsohon firayim minista Domingos Pereira, wanda Embalo ya kayar a zaben 2019.
Dias yace wannan yunkurin juyin mulkin na karya ne, an shirya shi ne kawai domin a hana bayyana shi a zaman wanda ya lashe zaben shugaban kasa.


