Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Amurka Tayi Barazanar Zata Rage Tallafin Da Take BayarwaSudan Ta Kudu, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Farashin Mai Ya Fadi Fiye Da Dala Daya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya Da Kasar Saudiya Sun Kulla Yarjejeniyar Tsaro Labarai
  • Gwamna Fubara Ya Koma Jam’iyar APC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Shugaba Tinubu Ya Gana Da Wasu Gwamnoni Shida Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Sojojin Najeriya Sun Kashe Fitaccen ’Yan Bindiga Kallamu A Jihar Sakkwato
Published: December 10, 2025 at 7:57 PM | By: Bala Hassan | Updated: December 11, 2025

Sojojin Najeriya Sun Kashe Fitaccen Shugaban ’Yan Bindiga, Kallamu, a Jihar Sokoto.

Sojojin Rundunar 8 Division ta Najeriya a Sokoto sun samu gagarumar nasarar kawar da fitaccen shugaban ’yan bindiga, Kachalla Kallamu, a yankin Sabon Birni, Jihar Sokoto.

An kashe Kallamu ne a wani samame na musamman da sojoji suka gudanar tare da hadin gwiwar ’yan sa-kai a yankin Kurawa, da safiyar Litinin.

Kallamu, wanda babban na hannun daman shugaban ’yan bindiga Bello Turji ne, ya kasance daya daga cikin wadanda suka addabi al’ummar Sabon Birni da hare-hare, garkuwa da mutane da kuma tada tarzoma a yankin.

Rahotonni sun bayyana cewa an kashe shi ne tare da daya daga cikin manyan masu samar wa Turji da kayan aiki da bayanan sirri, a wani artabu da ya faru da safiyar litinin.

Rahotanni sun ce Kallamu, wanda asalinsa daga Garin-Idi a Sabon Birni, ya dawo ne cikin yankin bayan tserewa wani farmaki da sojoji suka kai masa a watan Yunin 2025, inda ake zargin ya shige Kogi domin buya.

Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Post navigation

Previous Post: Shugaba Tinubu Ya Umarci Janye ‘Yan Sanda Masu Gadin Ministoci
Next Post: Abun Da Kuke Buƙatar Sani Game Da Gasar Cin Kofin Ƙasashen Afirka 2025

Karin Labarai Masu Alaka

“Hotuna” An Sako Daliban Makarantar St. Mary’s Su 100 Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
‘Yan-Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Daliban St. Mary! Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Sunayen Jakadu: Kungiyar CISLAC Ta Nemi A Janye Sunan Mr. Ayodele Oke Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Allah Ya Yi Wa Sheikh Dahiru Bauchi Rasuwa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
An Kubutar Da ‘Yan Matan Sakandire Su 24 Na Jihar Kebbi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
‘Yan-Ta’adda Sun Kara Sace Mutane A Jihar Naija! Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Ministan Tsaro Ya Umarci Janye Sojoji Daga Shingayen Bincike a Tituna
  • Atiku Ya Zargi Gwamnati Da Kama ‘Yan Adawa
  • Rashin Tsaro: Gwamnati Ta Bada Umarnin Daukar Ma’aikata Sama Da 94,000
  • Najeriya Ta Gabatar Da Tayin Karbar Bakuncin Wasannin Afirka Na 2031.
  • Mulkin Kama Karya Yazo Karshe a Kasar Bulgaria

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Rediyo
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Samar Da Tsaro A Jihar Kano Ba Sai An Sa Siyasa Ba! Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Liverpool Tayi Rashin Nasara A Wasanni Tara Wasanni
  • Bana Ba Harka Ga ‘Yan-Wasan Kwallon Kafar Najeriya Wasanni
  • Rasha: Zamu Ba Gwamnatin Venezuel Gudunmawa Sauran Duniya
  • Chelsea Tayi Kaca-Kaca Da Barcelona A Gasar UCL Wasanni
  • Shugaba Tinubu Ya Gana Da Wasu Gwamnoni Shida Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Rundunan  ‘Yan Sandan Jihar Bauchi, Ta Miƙa Miyagun Ƙwayoyi Da Ta Kama Wa NDLEA. Labarai
  • Gangamin Wayar Da Kai Don Kawo Karshen Cin Zarafin Jinsi A Jihar Gombe Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.