Ba’a ga wani canji na kirki ba farashin danyen mai a kasuwannin duniya, yayinda ake ciniki man kan farashi mafi tsada da ya kai wata bakwai bai kai haka ba, a yau talata, a dai dai lokacin da masu hada hadar man suke dakon labari dangane da shawarwari tsakanin Iran da Amurka kan shirin Nukiliyar kasar.
Farashin mai da ake kira Brent ya fadi da kamar centi 25 ya tsaya kan dala 71 da centi ashirin 24 kan ko wani ganga, yayinda mai mai da ake kira West Texas shima yayi baya da centi 25, ya tashi kan dala 66 da cent shida ko wace ganga.
Amurka da Iran dai za su yi zaman tattaunawa karo na uku dangane da shirin Nukiliyar Iran din a Geneva ranar Alhamis, kamar yadda aka ji daga ministan harkokin wajen Oman Badir Albusaidi ranar lahadi.


