Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Amurka Tayi Barazanar Zata Rage Tallafin Da Take BayarwaSudan Ta Kudu, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Farashin Mai Ya Fadi Fiye Da Dala Daya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Sojojin Najeriya Sun Kashe Fitaccen ’Yan Bindiga Kallamu A Jihar Sakkwato Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya Da Kasar Saudiya Sun Kulla Yarjejeniyar Tsaro Labarai
  • Gwamna Fubara Ya Koma Jam’iyar APC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Tinubu: Sojojin Mu Sun Yi Rawar Gani Don Kare Demokuraɗiyya A Jamhuriyar Binin
Published: December 7, 2025 at 10:13 PM | By: Bala Hassan | Updated: December 8, 2025

Shugaba Tinubu ya yaba wa sojojin Najeriya kan kare demokuraɗiyya a Jamhuriyar Binin.

Shugaba Bola Ahmad Tinubu, ya jinjinawa rundunar sojin ƙasar bisa gaggawar da ta yi wajen amsa kiran gwamnatin Jamhuriyar Binin domin taimakawa wajen kare tsarin mulkinsu na dimokuraɗiyya, bayan yunƙurin juyin mulki da aka yi a ƙasar da safiyar Lahadi.

A cewar fadar shugaban ƙasa, gwamnatin Binin ta aikawa Najeriya da buƙatu biyu na gaggawa, ta hanyar Ma’aikatar Harkokin Wajen ƙasar, tana neman a turo da jiragen yaƙin saman Najeriya domin kwace tasoshin da sojojin da suka yi juyin mulkin suka mamaye, ciki har da Talabijin na ƙasa da kuma wani sansanin soja.

Najeriya ta amsa wannan kira nan take, inda Shugaba Tinubu ya umarci rundunar sojin sama ta NAF ta shiga sararin samaniyar Binin domin kawar da barazanar.

Haka kuma gwamnatin Binin ta roƙi a tura ƙarin jiragen leƙen asiri da kuma sojojin ƙasa na Najeriya, domin taimaka musu a ayyukan tsaro da kariyar manyan cibiyoyin gwamnati a ƙarƙashin jagorancin hukumomin tsaron Binin.

Babban Hafsan Sojin Najeriya, Janar Olufemi Oluyede, ya tabbatar da cewa an kammala dukkan bukatun da ƙasar Binin ta nema, ciki har da zuwan sojojin Najeriya cikin ƙasar.

Yunƙurin juyin mulkin dai ya faru ne bayan wasu sojoji ƙarƙashin jagorancin Kanar Pascal Tigri sun mamaye gidan talabijin na ƙasar, inda suka bayyana cewa sun hambarar da gwamnatin Shugaba Patrice Talon tare da dakatar da muhimman hukumomin dimokuraɗiyya.

Sai dai da taimakon dakarun Najeriya, jami’an gwamnati masu biyayya ga Shugaba Talon sun kwace tashar Talabijin ɗin da sauran wuraren da aka mamaye, lamarin da ya kawo ƙarshen yunkurin juyin mulkin.

Da yake martani bayan tabbatar da dawowar tsarin dimokuraɗiyya, Shugaba Tinubu ya yaba wa sojojin Najeriya bisa rawar da suka taka.

“A yau, rundunar sojin Najeriya ta tsaya kai da fata wajen kare tsarin mulki a Jamhuriyar Binin bisa gayyatar gwamnatin ƙasar. Sun yi aiki bisa ka’idojin yarjejeniyar ECOWAS kan dimokuraɗiyya da kyakkyawan mulki,” in ji Shugaba Tinubu.

Ya ƙara da cewa Najeriya za ta ci gaba da goyon bayan gwamnati da al’ummar Binin wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciya hankali a yankin.

Labarai

Post navigation

Previous Post: Marc Brys: “Eto’o Baiyi Adalci Ga Onana, Da Vincent, Ba”
Next Post: Gwamnatin Tarayya Ta Samu Nasarar Ceto Wasu Daliban St. Mary’s

Karin Labarai Masu Alaka

Zamu Hada Kai Mu Yaki Cutar Shan’inna (Polio) Labarai
Tsohon Shugaban Brazil Bolsanaro Zai Tafi Gidan Yari Labarai
Guterres: Babban Kuskure Ne Yadda Isra’ila Ta Kai Farmaki A Gaza Labarai
Rwanda Tana Keta Yarjejeniyar Zaman Lafiya – Tshisekedi Labarai
Shugaba Tinubu: Naji Dadin Sako Daliban Neja Da Aka Sace Labarai
Gwannatin Jihar Kebbi Ta Arawa Maniyyata Kuɗin Aikin Hajji 2026, Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Ana Cigaba Da Jimamin Rasuwar Mataimakin Gwamnan Bayelsa
  • Bahagon Mancha Ya Buge Bahagon Maitakwasara Da Wasun Su!
  • Shirin Manuniya Yau Juma’a 12.12.2026
  • Ministan Tsaro Ya Umarci Janye Sojoji Daga Shingayen Bincike A Tituna
  • Atiku Ya Zargi Gwamnati Da Kama ‘Yan Adawa

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Tattalin Arzikin Najeriya Ya Karu A Karshen 2024 Rediyo
  • Jakadan Kasar Sin a Najeriya Ya Ziyarci Tinubu Najeriya
  • Gaza Ga Albarusai Ga Yunwa Tsaro
  • Chelsea Tayi Kaca-Kaca Da Barcelona A Gasar UCL Wasanni
  • Amurka Tayi Barazanar Zata Rage Tallafin Da Take BayarwaSudan Ta Kudu, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Bauchi Ta Amince Domin Inganta Kasuwancin Nama A Jihar Labarai
  • Gasar Cin Kofin Nahiyar Afrika A Wannan Makon Wasanni
  • Shirin Safe 0500 UTC Yau Litinin 11.17.2025 Rediyo
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.