Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • APC: Tinubu Da Shettima Za Su Sake Neman Wa’adi Na Biyu A 2027 Afrika
  • Sabuwar Sakatariyar Ƙungiyar Gwamnonin Arewa Za Ta Ƙarfafa Ayyukan Ci Gaban Yankin Afrika
  • TIC Dutse Ta Nemi Ƙarin Tallafin Gwamnatin Jigawa Don Faɗaɗa Ayyukanta Afrika
  • Gobara Ta Lalata Babban Zauren Majami’ar ECWA Gospel A Gombe Afrika
  • Gombe: ‘Yan Sanda Sun Tarwatsa Ƙungiyar Masu Fashi Da Damfara Ta Yanar Gizo Afrika

Tinubu: Sojojin Mu Sun Yi Rawar Gani Don Kare Demokuraɗiyya A Jamhuriyar Binin
Published: December 7, 2025 at 10:13 PM | By: Bala Hassan | Updated: December 8, 2025

Shugaba Tinubu ya yaba wa sojojin Najeriya kan kare demokuraɗiyya a Jamhuriyar Binin.

Shugaba Bola Ahmad Tinubu, ya jinjinawa rundunar sojin ƙasar bisa gaggawar da ta yi wajen amsa kiran gwamnatin Jamhuriyar Binin domin taimakawa wajen kare tsarin mulkinsu na dimokuraɗiyya, bayan yunƙurin juyin mulki da aka yi a ƙasar da safiyar Lahadi.

A cewar fadar shugaban ƙasa, gwamnatin Binin ta aikawa Najeriya da buƙatu biyu na gaggawa, ta hanyar Ma’aikatar Harkokin Wajen ƙasar, tana neman a turo da jiragen yaƙin saman Najeriya domin kwace tasoshin da sojojin da suka yi juyin mulkin suka mamaye, ciki har da Talabijin na ƙasa da kuma wani sansanin soja.

Najeriya ta amsa wannan kira nan take, inda Shugaba Tinubu ya umarci rundunar sojin sama ta NAF ta shiga sararin samaniyar Binin domin kawar da barazanar.

Haka kuma gwamnatin Binin ta roƙi a tura ƙarin jiragen leƙen asiri da kuma sojojin ƙasa na Najeriya, domin taimaka musu a ayyukan tsaro da kariyar manyan cibiyoyin gwamnati a ƙarƙashin jagorancin hukumomin tsaron Binin.

Babban Hafsan Sojin Najeriya, Janar Olufemi Oluyede, ya tabbatar da cewa an kammala dukkan bukatun da ƙasar Binin ta nema, ciki har da zuwan sojojin Najeriya cikin ƙasar.

Yunƙurin juyin mulkin dai ya faru ne bayan wasu sojoji ƙarƙashin jagorancin Kanar Pascal Tigri sun mamaye gidan talabijin na ƙasar, inda suka bayyana cewa sun hambarar da gwamnatin Shugaba Patrice Talon tare da dakatar da muhimman hukumomin dimokuraɗiyya.

Sai dai da taimakon dakarun Najeriya, jami’an gwamnati masu biyayya ga Shugaba Talon sun kwace tashar Talabijin ɗin da sauran wuraren da aka mamaye, lamarin da ya kawo ƙarshen yunkurin juyin mulkin.

Da yake martani bayan tabbatar da dawowar tsarin dimokuraɗiyya, Shugaba Tinubu ya yaba wa sojojin Najeriya bisa rawar da suka taka.

“A yau, rundunar sojin Najeriya ta tsaya kai da fata wajen kare tsarin mulki a Jamhuriyar Binin bisa gayyatar gwamnatin ƙasar. Sun yi aiki bisa ka’idojin yarjejeniyar ECOWAS kan dimokuraɗiyya da kyakkyawan mulki,” in ji Shugaba Tinubu.

Ya ƙara da cewa Najeriya za ta ci gaba da goyon bayan gwamnati da al’ummar Binin wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciya hankali a yankin.

Labarai

Post navigation

Previous Post: Marc Brys: “Eto’o Baiyi Adalci Ga Onana, Da Vincent, Ba”
Next Post: Gwamnatin Tarayya Ta Samu Nasarar Ceto Wasu Daliban St. Mary’s

Karin Labarai Masu Alaka

Akwai Bukatar APC Tayi Gyare-Gyare Kafun Zabe Afrika
“Yan Wasan Super Eagles Sun Karbi Alkawarin Da Gwamnati Tayi Musu AFCON 2023 Labarai
Amurka Ta Cire Takunkumin Da Ta Kakabawa Shugaban Venezuela Amurka
Sarakunan Gombe Da Zazzau Sun Yi Kira Ga ‘Yan Najeriya Su Rungumi Haɗin Kai Da Zaman Lafiya Afrika
Zulum Ya Rushe Majalisar Zartarwa Ta Jihar Borno Afrika
Tarkacen Makamai Masu Linzami Sun Lalata Gidaje Da Wuraren Kasuwancin Palasdinawa Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • APC: Tinubu Da Shettima Za Su Sake Neman Wa’adi Na Biyu A 2027
  • Sabuwar Sakatariyar Ƙungiyar Gwamnonin Arewa Za Ta Ƙarfafa Ayyukan Ci Gaban Yankin
  • TIC Dutse Ta Nemi Ƙarin Tallafin Gwamnatin Jigawa Don Faɗaɗa Ayyukanta
  • Gobara Ta Lalata Babban Zauren Majami’ar ECWA Gospel A Gombe
  • Gombe: ‘Yan Sanda Sun Tarwatsa Ƙungiyar Masu Fashi Da Damfara Ta Yanar Gizo

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Kasar Morocco Ta Kwashe ‘Yan Kasar Daga Sassan Ambaliyar Ruwa Afrika
  • ‘Yan-Ta’adda Sun Yi Ma Wasu Mutane Yankan Rago A Jihar Neja Labarai
  • Prime Ministan Senegal Ya Bayyana Shirin Sauya Sheka Afrika
  • APC Ta Ayana Tsohon Gwamnan Bauchi M.A Abubakar A Matsayin Dan Takarar Gwamna Afrika
  • Amurka Ta Baiwa Najeriya Wasu Muhimman Kayan Yaki Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya: Ta Aiwatar Da Tsarin Ba Aiki Ba Albashi Ga Ma’aikata Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Benue Da MACBAN Sun Kai Ziyarar Ta’aziyya Ga Iyalan Marigayi Ardo Risku Mohammed Afrika
  • Babban Malamin Musulunci Sheikh Usman Kusfa Zaria Ya Rasu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.