Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Najeriya Taja Hankalin ‘Yan Najeriya Mazauna Iran Da Kasashen Larabawa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnan Gombe Yace An Sace Yara 48 A Jihar Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • ‘Yan Bindiga Suna Cigaba Da Kashe Mutane A Garin Gwana Dake Jihar Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Tsofin Shugabanin Kasa Sun Karbi Bakoncin Hafsan Sojin Najeriya
Published: January 6, 2026 at 8:27 PM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: January 7, 2026

Babban hafsan sojin ƙasan Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya kai ziyarar girmamawa ga tsofaffin shugabannin ƙasa, Janar Ibrahim  Badamasi Babangida da Janar Abdulsalami Abubakar, tare da ziyartar Gwamnatin jihar Neja, domin ƙarfafa haɗin gwiwar farar hula da sojoji da inganta tsaro.

Ziyarorin, da suka gudana a Minna, sun nuna ƙudirin rundunar sojin ƙasa na inganta horo, shirye-shiryen aiki da haɗin kai da shugabannin siyasa da gwamnatocin jihohi wajen fuskantar ƙalubalen tsaro.

Shaibu ya bayyana muhimmancin jihar Nijar a tsarin tsaron ƙasa, yana mai cewa rundunar na amfani da dukkan albarkatu da fasaha domin magance matsalolin tsaro.

Ya kuma kai ziyarorin aiki ga Rundunonin 31 da 11 da 18 a Bida domin tantance kalubalen aiki da ƙarfafa rundunonin da ke bakin aiki.

A Mayar Da Jawaban su, Babangida da Abdulsalami sun yaba da jagorancin Shaibu, tare da yi masa addu’ar samun nasara yayin da yake jagorantar Rundunar Sojin ƙasa ta Najeriya.

Tsaro

Post navigation

Previous Post: Na Duke Tsohon Ciniki
Next Post: Kotu Ta Bada Belin Abubakar Malami Bisa Wasu Sharruda

Karin Labarai Masu Alaka

Sojoji Sun Fatattaki ‘Yan Ta’adda A Borno Tsaro
Shugaba Trump Yace Bazai Bari Iran Ta Mallaki Nukiliya Ba Amurka
An Hana Yada Rahotannin Siyasa A Kasar Uganda Tsaro
Amurka Zata Aika Jiragen Yaki Biyu Gabas Ta Tsakiya Amurka
Ana Zargin Wani Dan Kasar Libya Da Fataucin Mutane Tsaro
An Kashe Sojojin Bangladesh A Kasar Sudan Tsaro

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ‘Yan Uwa Musulmi A Jihar Gombe Sunyi Allah Wadai Da Kisan Ayatollah Khomeini
  • An Samu Kaburbura Biyu Dauke Da Gawarwaki 173 A Kasar Kwango
  • Yan Bindiga Suna Cigaba Da Kashe Mutane A Garin Gwana Dake Jihar Bauchi
  • Karancin Iskar Gas Kalubale Ne Ga Wutar Lantarki
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Asusun IMF Zai Bawa Kasar Misra Lamunin Sama Da Dala Biliyan 2 Sauran Duniya
  • Shugaban Trump: Washington Zatayi Cinikayya Da Indiya Amurka
  • Mun Kwato Kimanin Naira Biliyan 40 Na Badakala A Tsawon Shekara Daya Labarai
  • Tinubu Yace Zayyi Hadaka Da Kasashen Duniya Domin Kawo Karshen Rashin Tsaro. Najeriya
  • Gwamnatin Najeriya Ta Ayyana Ranakun Hutu Najeriya
  • Babangida: Hakika Abiola Ya Lashe Zaben Watan Yuni 1993 Labarai
  • An Sako Ɗaliban Makaranta 130 Da Aka Sace A Jihar Neja  Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • ‘Yan Bindiga Sun Kashe Fiye Da Mutane 50 Tare Da Sace Mata Da Yara A Jihar Zamfara Najeriya
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.