Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Najeriya Ta Dauki Hayan Amurkawa Don Kyautata Alaka Da Trump Game Da Kisan Kiristoci Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Tarayya Ta Cimma Yarjejeniya Da Kungiyar Malaman Jami’oi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Amurka Ta Baiwa Najeriya Wasu Muhimman Kayan Yaki Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Trump Yayi Kira Ga ‘Yan Ƙasar Iran Su Ci Gaba Da Zanga Zanga Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Syria: Mutane Sun Yi Zanga Zanga Domin Nuna Rashin Amincewa Da Korar Kurdawa A Birnin Aleppo Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Yau Litinin Za’a Mika Daliban Ga Iyayen Su
Published: December 22, 2025 at 5:06 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Kakakin shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya, yace an sako sauran dalibai 130 da aka sace daga wata makaranta ta ‘yan Katolika a jihar Neja, daya daga cikin sace-sacen mutane mafi muni da aka gani a kasar cikin ‘yan shekarun nan.

Bayo Onanuga ya fada cikin wata sanarwar da ya fitar a shafin X cewa an sako sauran dalibai 130 da ‘yan ta’adda suka sace, yana mai fadin cewa a yau litinin ake sa ran zasu isa Minna, babban birnin Jihar Neja, kuma zasu koma cikin ‘yan’uwansu domin suyi bukukuwan kirsimeti tare.

Mr. Onanuga yace daliban su samu ‘yan cinsu ne a bayan wani mataki na soja da jami’an leken asiri.

Daliban suna daga cikin yara fiye da 300 da malamai 12 da ‘yan bindiga suka sace daga makarantar St Marys Catholic dake garin Papiri da asubahin ran 21 ga waran Nuwamba.

Sace daliban ya haddasa fusata kan yadda rashin tsaro yake kara yin muni a yankin arewacin Najeriya, inda ‘yan bindiga ke kai hare-hare kan kauyuka da garuruwa da ma makarantu suna sace mutane don neman a biya su kudin fansa.

Labarai

Post navigation

Previous Post: An Sako Ɗaliban Makaranta 130 Da Aka Sace A Jihar Neja 
Next Post: Hari Akan Wata Mashaya Ya Rutsa Da Mutane 9 A Afirka Ta Kudu

Karin Labarai Masu Alaka

‘Yan-Ta’adda Sun Yi Ma Wasu Mutane Yankan Rago A Jihar Neja Labarai
Kamfanin Hakar Ma’adanai Na Kasar Kanada Ya Cigaban Da Aikinsa Labarai
Sojojin Kasar Isra’ila Sun Kashe Wani Babban Kwamandan Hamas Labarai
Mizanin Tattalin Arzikin Najeriya Na 2024 Ya Karu Da Kashi 3.84% Labarai
Gwamnatin Bauchi: Ba Zamu Bude Makarantu Ba Sai 2026 Labarai
Kotun Kasar Rasha Ta Daure Dan Kasar Belarus Shekarar 22 A Kurkuku Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Najeriya Ta Dauki Hayan Amurkawa Don Kyautata Alaka Da Trump Game Da Kisan Kiristoci
  • Gwamnatin Tarayya Ta Cimma Yarjejeniya Da Kungiyar Malaman Jami’oi
  • Kabiru Vice: Najeriya Zata Iya Nasara A Kan Moroko AFCON 2025.
  • Motar Yashi Ta Kashe Mutane Shida A Wani Coci Dake Legas
  • An Kaddamar Da Rijistar Zamani Ta Zamowa Mamba A Jam’iyar APC

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • An Gudanar Da Addu’o’i Na Musamman Don Neman Zaman Lafiya Labarai
  • Ana Cigaba Da Tattaunawa Tsakanin Trump Da Zelensky Domin Tsagaita Wuta A Ukraine Labarai
  • Sabon Ma’aikacin Tsaro Ne Ya Kashe Amurkawa Amurka
  • Kocin Ranchers Bees Ya Yi Murabus Wasanni
  • Isra’ila Ta Dau Alwashin Kawo Karshen Falasdi Labarai
  • Zelensky Na Ukraine Zai Gana Da Takwaransa Na Faransa A Yau Labarai
  • Bana Ba Harka Ga ‘Yan-Wasan Kwallon Kafar Najeriya Wasanni
  • Lauya Bala: Tabbas Kotu Zata Soke Zaben Shugaban PDP, Turaki Najeriya
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.