Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Shugaba Tinubu Yakarawa Mambobin ASUU Kashi 40 Na Albashi
Published: December 25, 2025 at 7:30 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya wayo (ASUU) ta nuna farin ciki bayan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta amince da ƙarin albashi da kashi 40 cikin 100 ga malaman jami’o’i, biyo bayan nasarar sake tattaunawa kan yarjejeniyar 2009 da aka kulla tsakanin ASUU da gwamnatin tarayya.

ASUU ta sanar da cewa an cimma yarjejeniyar ne a ranar 23 ga Disamba, 2025, lamarin da ya kawo ƙarshen tattaunawar da ta shafe shekaru takwas ana yi tun daga 2017.

Tsawon lokacin tattaunawar ya biyo bayan gazawar gwamnatin tarayya wajen duba yarjejeniyar 2009 a shekarar 2012, abin da ya jawo yawan yajin aiki a tsawon shekaru.

A wata sanarwa da aka fitar a ranar 24 ga Disamba, 2025, ƙungiyar ta ce sabuwar yarjejeniyar an tsara ta ne domin farfaɗo da tsarin jami’o’in gwamnati a Najeriya ta hanyar magance matsaloli da suka daɗe suna addabar fannin, kamar ƙarancin kuɗaɗen tallafi, ‘yancin kai na jami’o’i, ‘yancin gudanar da karatu da kuma karuwar ƙauracewar ƙwararru.

Baya ga ƙarin albashin, yarjejeniyar ta kuma ƙunshi inganta sharuddan aiki, sake tabbatar da tanadin fansho ga farfesoshi, sabon tsarin kasafin kuɗi na musamman ga jami’o’i, da kuma shawarwarin kafa Hukumar Bincike ta Ƙasa wacce za a rika tallafa mata da aƙalla kashi ɗaya cikin 100 na tattalin arzikin Najeriya.

Najeriya

Post navigation

Previous Post: Fadar Shugaban Ƙasan Najeriya Ta Musanta Wani Labarin ƙarya
Next Post: Harin Bom Din Maiduguri Ya Kashe Mutane Biyar Ya Raunata Fiye Da Talatin

Karin Labarai Masu Alaka

Gombe Ta Ƙarfafa Matasa da Ƙwarewar da Za Ta Kai Su Masana’antar Mai Da Iskar Gas Afrika
‘Yan Sanda Sun Kama Mutane 33 Bisa Zargin Kai Hari A Jihar Kwara Afrika
Mabiya Dariqar Tijjaniyya Sunfara Gudanar Da Addu’oi Saboda Tsare Sheikh Sani Khalifa Zariya Afrika
Yawan wadanda suka mutu a mummunan harin yanbindiga a Jihar kwaran Najeriya yakai 170 Najeriya
‘Yan Sandan Gombe Sun Fara Kama Motocin Da Ba Su Da Lambar Rajista ko Masu Boye Lambobinsu Afrika
Gwamnatin Gombe Ta Aza Tubalin Gina Sakatariyar Gundumomin Cigaba (LCDAs) Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Najeriya Da Dubai Zasu Karbi Bakoncin Taron Zuba Hannayen Jari Najeriya
  • Tinubu Ya Lashe Zaɓen Fidda Gwanin APC Da Kuri’u Miliyan 11 Afrika
  • An Kashe Falatsinawa Biyar A Wani Hari Da Isra’ila Takai Wata Makaranta A Gaza Tsaro
  • An Bude Gasar Bauchi Annual International Polo 2026 Wasanni
  • Kasar Ghana Ta Tono Gold Na Miliyoyin Kudade Kimiya
  • FIFA Ta Yi Wa Malaysia Kaca-kaca Wasanni
  • Shahararren Dan Dambe Anthony Joshua Yayi Hatsarin Mota A Jihar Ogun Labarai
  • Isra’ila Ta Zantar Da Hukuncin Kisa Ga Masu Kai Hare Hare Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.