Ranar Lahadi idan Allah ya kai mu ake sa ran mutane a Myanmar za su gudanar da zabe, yayinda kasar take fama da yaki, wadda ya haifar da mummunar yanayin rayuwa a yankin Asiya.
Kasar wacce take cikin kasashe mafiya talauci a yankin kudu maso gabashin asiya, tana fama da fitina mai tsanani sakamakon juyin mulkin da dakarun kasar suka yi wa gwammnatin farar hula karkashin jagorancin an san Su shi dai ta sami lambar yabo ta Nobel.
Myanmar tana fuskantar yanayin rayuwa mafi tsanani a Asiya sakamakon ci gaba da yaki da ake yi a kasar da kuma bala’o’i ciki harda mummunar girgizar kasa da kasar ta fuskanta cikin watan Maris na bana.
A baya dai mahukuntan soja a kasar suna danne rahotanni da suke nuna matsalar yunwa a kasar, inda take hana masu bincike yin nazarin karancin abinci, tareda hana kungiyoyin agaji bayyana rahotannnin, baya ga hana ‘yan jarida walwala a kasar tun bayan da sojojin suka yi juyin mulki.
Myanmar tana daga cikin kasashe da basa samun tallafi a fadin duniya, inda MDD tace kashi 12 cikin dari na gudumawar da ake bukata domin allafawa kasar ne aka samu.


