Masu ruwa da tsaki akan Lamurran siyasa sun fara maida Martani akan matakin da Ministan Labaran Najeriya da wayar da kan Jama,a Idris Malagi na korar daya daga cikin ma,aikatansa saboda dalilai na siyasa.
Da tsakiayar ranar wannan larabace dai mataimakin na musamman akan yada Labarai ga Minista Malagi Malam Rani,u Ibrahim ya fitar da Wata sanarwar cewa Ministan ya Dakatar da Daya Daga cikin Ma,aikatansa Mai Suna Sa,idu Enagi Saboda ya fitar da Wani bayani a Kafar yada Labarai na sada zumunta dake Nuna Ministan ya shirya tsaf Domin takarar Gwamnan Jihar Neja a 2027.
Malam Sa,idu Etsu tsohon Dantakarar shugaban cin Jam,iyyar APC a Najeriya yace matakin da Ministan ya dauka yayi Dai dai fomin yanzu lokaci baiyi ba.
Shima dattijon siyasa a Jihar Neja Alh.Awaisu Giwa Kuta yace matakin da Ministan Labaran ya dauka yayi dai dai domin yanzu Jihar Neja zaman makoki akan fotinar Yan ta,adda ba wai batun neman mukamin siyasa ba.
To sai jigon Jam,iyyar PDP mai adawa a Najeriya Hon.Yahaya Ability yace akwai kuskure Babba da ministan ya tabka a dai dai wannan zamani na siyasa duk da cewa Jihar Nejan na cikin Yanayi na masifar yanbindiga.
Azaben Shekara ta 2023 Malagi yayi takara gwamnan Jihar Neja a jam,iyyar APC inda gwamna Umar Bago ya kadashi a zaben fidda gwani.Martanin wasu Yan Najeriya ga Ministan Labarai akan korar hadiminsa.


