A Syria, ko Sham, dubban mutane ne suka yi zanga zanga cikin ruwan sama, a arewa maso gabashin kasar, domin nuna rashin amincewar su da korar mayakan kurdawa daga birnin Aleppo a makon jiya, bayan kwanaki da aka yi ana gwabza fada.
Tarzomar a Aleppo ta zurfafa rashin fahimtar juna a kasar, da shugabanta na yanzu Ahmed alshara’a yayi alwashin hada kan kasar, mataki da yake fukantar turjiya daga kurdawa wadanda suke dari dari da gwamnatinsa, mai sigar addini,
Ma’ikatar kiwon lafiya a Syria ko Sham tace fadan na tsawon kwanaki biyar ya kashe mutane 23, mutane fiyeda dubu dari da hamsn suka tsere daga unguwanni da suke hanun kurdawa. Wani jami’in kurdawa Ilham Ahmed ya fadawa manema labarai yau Talata cewa, mutane 48 suka halaka sakamakon farmakin da dakarun kasar suka kai musu. Sai dai kamfanin dillancin labarai na Reuters bai tantance sabanin dake akwai tsakanin alkaluma da gwamnati da kuma kurdawan suka bayar ba.


