Shugaban kungiyoyin Magoya Bayan Kwallon Kafa ta Najeriya reshen jihar Bauchi Alh Kabiru Ahmed Vice ya ce Najeriya zata iya samun nasara akan Ƙasar Moroko AFCON 2025.
Alh Kabiru Ahmed Vice ya ce la’akari da yadda tawagar Najeriya suka taka rawar gani a Wasanni su na baya a gasar cin kofin kasashen Afirka tun daga matakin rukuni har zuwa kwata final, haka na nuna cewar zata iya doke masu masaukin baki ƙasar Moroko a wasan da zasuyi na dab da Karshe.
Dukkanin Ƙasashen Afirka da suka je gasar babu wacce ta jefa yawan kwallaye a raga kamar Super Eagles, ” in ji shi.
Wannan ya na da nasaba da irin hazikan yan wasa da suke da su wadda suke fafata a manyan kungiyoyin kwallon kafa ta kasashen turai cikin su hadda wadda suka taba zama Gwarzayen kwallon kafa na afirka guda 2, Victor Osimhen da Ademola Lookman, ganinsu ya kara wa wasu ‘yan wasan karfin guiwa.
Ya ce duk da cewa Ƙasar Moroko ita ce mai masaukin baki ta na da dubban magoya baya a filin hakan ba zai ba ‘yan wasan Najeriya tsoro ba saboda sun goge da irin wannan abu tun a Turai.
Har ila Yau Kabiru yayi kira ga hukumar kwallon kafa ta Najeriya da ta rinka kulawa da walwalan ‘yan wasa da magoya baya don hakan shine zai kara musu kwarin guiwar yin abunda ya dace.
Duk da cewa wannan karon hukumar kwallon kafa ta Najeriya bata mara baya wa bangaren magoya baya don zuwa gasar cin kofin kasashen Afirka da ke guda na a kasar Moroko ba amman suna iya abun da zasuyi don ganin an samu nasara in ji Kabiru.
Saboda haka yayi kira ga gwamnati da masu hanu da shuni da su rinka tallafawa wajan ganin magoya baya suna hallartar irin wa’yannan gasar.
Daga karshe yayi fatan Najeriya zata lashe wannan kofin kasashen Afirka don huce haushin rashin zuwa gasar cin kofin Duniya.
A yau Laraba ne Ƙasar Najeriya zata buga da ƙasar Moroko a matakin wasan dab da Karshe na gasar cin kofin kasashen Afirka AFCON 2025, da ke gudana a can Moroko.


