Shugaba Yoweri Museveni na Uganda yana kokarin tsawaita zamansa kan kujerar shugabancin kasar zuwa shekaru hamsin da wani abu, a zaben da za a gudanar yau alhamis bayan da aka tsinke akasarin hanyoyin sadarwa na intanet.
Ana sa ran Museveni mai shekaru 81 da haihuwa zai samu galaba a kan babban abokin hamayyarsa, mawaki mai suna Bobi Wine, amma ana daukar wannan kuri’a ta yau alhamis a matsayin wadda zata gwada ko yana da karfin tasirin siyasar da zai iya kauce ma fitinar zabe da aka gani a makwabtansa Kenya da Tanzaniya.
Shugaban da ya jima sosai a kan karagar mulki yayi kamfe da manufar kare ci gaban da ya kawo kasar, yana mai alkawarin wanzar da zaman lafiya da kawar da talauci.

Bobi Wine mai shekaru 43 da haihuwa, yayi alkawarin kawo karshen abinda ya kira mulkin kama karya na Museveni, inda ya maida hankali wajen janyo ra’ayoyin matasa da suka rasa aikin yi. Fiye da kashi 70 cikin 100 na al’ummar Uganda matasa ne ‘yan kasa da shekara 30 da haihuwa.


