Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Inuwa Ya Bukaci A Kara Zuba Jari A Ilimin Sana’o’i Domin Samar Wa Matasa Aikin Yi Afrika
  • Gwamnonin Arewa Sun Yi Jimamin Rasuwar Bamanga Tukur, Sun Yaba Da Gudunmawarsa Ga Najeriya Afrika
  • Tsohon Shugaban PDP, Bamanga Tukur, Ya Rasu Yana da Shekaru 91 Afrika
  • Filato: Gwamnati Ta Ƙarfafa Matakan Kariya Yayin Sake Buɗe Makarantu Afrika
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika

Kasar Amurka Da Denmark Suna Rikici Akan Iyakar Greenland
Published: January 15, 2026 at 4:05 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Wani babban jami’in kasar denmark, yace har yanzu akwai abinda ya kira “babban sabani mai tushe a tsakaninsu da shugaba Donald Trump na Amurka a game da yankin Greenland, a bayan tattaunawar da suka yi a fadar White House da mataimakin shugaban Amurka JD Vance da sakataren harkokin waje Marco Rubio.

Amma kuma sassan biyu sun yarda zasu kafa wani kwamitin hadin guiwa domin tattauna hanyoyin warware sabanin da suke da shi a yayin da shugaba Trump ya ci gaba da nacewa a kan lallai sai dai Amurka ta karbi wannan yanki mai karamin ikon cin gashin kai daga hannun kawarta na kungiyar kawancen tsaron NATO, Denmark.

Trump ya yana kokarin nuna cewa ya kamata NATO ta taimaka ma Amurka wajen mallakar wannan tsibiri da ya fi kowanne girma a duniya, yana mai fadin cewa ba zai yarda da duk wani abinda zai gaza komawar yankin na Greenland hannun Amurka baki dayansa ba.

A halin da ake ciki, kasar Denmark ta bayyana shirye shiryen bunkasa yawan sojojinta a yankin tekun Arctic da arewacin tekun Atlantika a yayin da Trump yake wannan kokari nasa na mallakin Greenland.

Amurka

Post navigation

Previous Post: Kasar Sham Ta Sallami Wasu Fararen Hula
Next Post: Amurka Ta Janye Sojojinta Daga Gabas Ta Tsakiya

Karin Labarai Masu Alaka

Kasashen Yankin Gulf Sun Bukaci Amurka Takawo Karshen Iran Afrika
Shugaba Trump Yace Amurka Zata Janye Yaki Da Iran Afrika
Amurka Ta Janye Sojojinta Daga Gabas Ta Tsakiya Amurka
Kasashen Yankin Gulf Sun Bada Sanarwa Afrika
Wani Bincike Ya Nuna Cewar Da Wuya Iran Ta Bude Mashigin Hormuz Afrika
Rundunar Sojin Amurka Zasu Kaiwa Iran Hari Amurka

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Inuwa Ya Bukaci A Kara Zuba Jari A Ilimin Sana’o’i Domin Samar Wa Matasa Aikin Yi
  • Gwamnonin Arewa Sun Yi Jimamin Rasuwar Bamanga Tukur, Sun Yaba Da Gudunmawarsa Ga Najeriya
  • Tsohon Shugaban PDP, Bamanga Tukur, Ya Rasu Yana da Shekaru 91
  • Filato: Gwamnati Ta Ƙarfafa Matakan Kariya Yayin Sake Buɗe Makarantu
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • An Samu Kaburbura Biyu Dauke Da Gawarwaki 173 A Kasar Kwango Afrika
  • Katsina United Ta Yi Jimamin Mutuwar Ɗan Wasanta Ozoh Wasanni
  • Shugaba Donald Trump Ya Nada Shugaban Bankin Tarayya Amurka
  • Lawal, Filin Wasa Na Rashidi Yekini Ko Turai Iyaka Wasanni
  • Dan Wasan Gaba Na Manchester United, Zirkzee Ya Amince Da Komawa Juventus Ko Napoli Wasanni
  • Chelle: Rashin Jituwa Tsakanin Osimhen Da Lookman Matsala Ce Ta Cikin Gida Wasanni
  • ‘Yan Sanda A Gombe Sun Jaddada Shirin Yaƙi Da Munanan Dabi’u Afrika
  • Farashin Mai A Kasuwannin Duniya Yayi ƙasa Kadan Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.