
Mizanin karfin tattalin arzikin Najeriya a rubu’in karshe na shekara ta 2024 ya karu da kashi 3.84% daga kashi 2.74% a 2023.
Hukumar kididdiga ta Najeriya NBS ta saki rahoton da ya nuna sassan da ke waje da danyen man fetur ne ke kan gaba wajen raya arzikin.
“Masu neman bayani kan mizanin farashi CPI sun sauke rahoton fiye sau dubu 500 a shekara 6 da ta wuce. Don haka wannan rahoto da na mizanin arziki GDP ya zama mai muhimmanci da mu ke fitarwa bisa bin ka’idoji na duniya” Inji shugaban hukumar kididdigar Prince Adeyemi Adeniran.
Alkaluman sun nuna bangaren sufurin jirgin kasa, mota, sadarwa da cibiyoyin kudi na kan gaba wajen karfin hada-hadar arziki a Najeriya.
Babban jami’I na hukumar ta NBS Ibrahim Yakubu Tanko ya yi karin haske da nuna mizanin na GDP ya na duba dukkan hada-hada ce ta kudi kuma a kan sabuta shi bisa tafiyar zamani “akwai sana’o’I da a da ba mu sa su ba kamar harka na yanar gizo. Ga kuma harka ta sufurin yanar gizo kamar UBER da kasuwancin JUMI’A, wadannan hanyoyi sun yi karfi don a wasu kasashen ma su ne hanyoyin kasuwancin”
A nan hukumar ta NBS ta yi karin bayani kan mizanin farashin kaya CPI da wasu kafafen labaru su ka yi kuskuren fahimtar rahoton da ba wai ya na nuna saukowar farashi ba ne daga kashi 34% zuwa 28.4% amma sauya shekarar da a ke gwada lissafin tsada daga 2009 zuwa 2024 ya kawo bambancin bisa ma’anar yanzu a kan gwada ma’aunin ne daga bara inda dama kaya sun yi tsada.
Kwarerre a fannin mizanin farashi Dokta Abdullahi Jibrin ya duba amfanin mizanin tun da ba ya na nuna saukar farashi a kasuwa ba ne “idan gwamnati za ta daidaita albashi ta na amfani da wannan hauhawa ne. Babban banki kan yi amfani da alkaluman wajen karawa ko rage kudin ruwa. Talakawa ma kan yi amfani da ma’aunin wajen sarrafa kudin su”
NBS ta saki rahoton mizanin farashi da na tattalin arziki daidai lokacin da kayan masarufi su ka dan sauka a kasuwa wanda ke da alaka da shigo da abinci daga ketare da kuma kara darajar canjin Naira kan dalar Amurka.