Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

‘Yan Sandan Jihar Bauchi Sun Kama Wasu Matasa da Ake Zargin Su Da Sara Suka 
Published: January 19, 2026 at 9:28 AM | By: Bala Hassan

Rundunan ‘Yan Sandan Jihar Bauchi Ta Kama ‘Yan Sara Suka

An Kama ‘Yan Ta’adda Goma Sha Huɗu (‘Yan Sara-suka) a lokacin wani samame a Bauchi.

Rundunan ta ‘yan sandan jihar Bauchi da ke arewa maso gabas a Najeriya tace a ranar 15 ga Janairu 2026 da misalin ƙarfe hudu da rabi na yammaci, wata sashin sintiri ta yi aiki na kai-kawo kan ayyukan ‘yan ta’adda (‘Yan Sara-suka) a anguwanin Bakaro, Kofar Dumi, Tudun Yarima da Karofin Madaki.

Bayan samun rahoton leken asiri na sirri, jami’in ‘yan sanda na ‘A’ Division Bauchi CSP Hassan A. Musa ya jagoranci wata tawaga da gaggawa inda ya ya cafke wadanda ake zargi da aikata wannan aika-aika, kamar yadda Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan jihar SP Nafiu Habib, ya bayyana a madadin kwamishinan ‘yan sandan jihar Bauchi Sani Omolori Aliyu.

Wa’yanda aka kama sune.

1. Malam Abbati mai shekaru 20,

2. Malam Mamman mai shekaru 21,

3. Malam Adamu dan shekaru 22,

4. Malam Khalid mai shekaru 20,

5. Malam Abubakar mai shekaru 19,

6. Mr. Mahmood dan shekaru 22,

7. Malam Jabir mai shekaru 21,

8. Malam Haruna mai shekaru 18,

9. Malam Khalid mai shekaru 18,

10. Malam Abubakar dan shekaru 19,

11. Malam Kabiru mai shekaru 20,

12. Malam Anas mai shekaru 20,

13. Malam Mohammed dan shekaru 19,

14. Abdulkarim mai shekaru 22,

Duk kansu daga unguwar Kofar Dumi, Karofin Madaki, Tudun Yarima, da Bakaro, a Bauchi

Wadanda ake zargin sun amsa laifinsu na hada baki a tsakaninsu, inda suke dauke da makamai masu hatsarin gaske da suka hada da wukake masu kaifi, da makamantansu, inda suka mamaye yankunan suka kai musu hari da duka ga al’uma ma zauna unguwar da aka ambata, tare da kwace musu wayoyin hannu da kudi, sannan suka raunata duk wanda ya ki mika musu.

Kwamishinan ‘yan sanda, CP Sani-Omolori Aliyu, ya yabawa al’umar jihar Bauchi bisa hadin kai da goyon bayan da su ke bayarwa, wajan kawo rahoton bata gari, sannan ya karfafa musu gwiwa da su kasance masu taimaka wa jami’an tsaro wajan sanya ido ga masu aikata miyagun hali

Labarai

Post navigation

Previous Post: Kasar Sham Ta Sanar Da Tsagaita Wuta Tsakaninta Da Kungiyar Kurdawa
Next Post: Mutum Mafi Tsufa A Saudiyya Ya Rasu Yana Da Shekaru 142

Karin Labarai Masu Alaka

Kasar Amurka Tabada Tabbacin Bawa Ukraine Tsaron Shekarun 15 Amurka
Iran Zata Kai Hari Tashar Makamashin Ruwa A Gulf Afrika
‘Yan Tada Kayar Baya Sun Tayar Da Bom A Maiduguri Labarai
Thailand Da Cambodia Sun Fara Tattauunawa Kan Batun Tsagaita Wuta Labarai
Gwamnatin Najeriya Ta Tura Mutane 386 Gidan Yari Afrika
Gwamnatin Tarayya Za Ta Sake Fasalin Shirin NYSC Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Kotu A Abuja Tabawa Goodluck Jonathan Daman Tsayawa Takara Afrika
  • Tawagar Masu Yi Wa Maniyyata Hidima Za Ta Tashi Zuwa Saudiyya Afrika
  • Wakilan Majalisar Dokokin Phillipines Suna Yunkurin Tsige Shugaban Kasar Afrika
  • Harin Makami Mai Linzami Da Rasha Ta Kai Yayi Barna Sosai A Ukraine Afrika
  • An Kusa Kawo Karshen Matsalolin Tsaro A Jihar Filato Afrika
  • Ƙungiyoyin Premier 17 Za Su Rasa ‘Yan Wasa 40 saboda Gasar AFCON 2025, Wasanni
  • An Bude Gasar Bauchi Annual International Polo 2026 Wasanni
  • Shugaba Tinubu: Naji Dadin Sako Daliban Neja Da Aka Sace Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.