Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Babban Hafsan Tsaron Najeriya Ya Gargadi Masu Tayar Da Hankali
Published: January 24, 2026 at 9:24 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Babban Hafsan Sojin Ƙasarln Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya yi gargaɗi mai tsanani ga masu aikata laifuka da ke tayar da hankalin al’umma a faɗin ƙasar, inda ya ce za su fuskanci ƙarfin sojoji matuƙar ba su tuba daga munanan ayyukansu ba.

Fiye da sojojin musamman dubu ɗaya (1,000) ne aka ƙara tura wa fagen yaƙi domin ƙarfafa ayyukan tsaron cikin gida da ake gudanarwa a sassa daban-daban na ƙasar.

Babban Hafsan Sojin ya bayyana hakan ne yayin bikin kammala atisayen Exercise Restore Hope 9 da aka gudanar a sansanin rundunar sojin Najeriya da ke Kachia.

Ya jaddada cewa rundunar sojin ƙasa za ta ci gaba da tinkarar duk wani ɓangare na masu tada fitina, inda ya ce duk masu aikata laifi za su gamu da ƙarfin da za su iya jurewa, har sai sun daina munanan ayyukansu kuma sun tuba.

Ya kuma tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa rundunar sojin ƙasa za ta ci gaba da jajircewa wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Najeriya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Gwamna Ododo Ya Gargadi Sarakunan Gargajiya
Next Post: Najeriya Da Amurka Sun Amince Su Haɗa Kai Don Inganta ’Yancin Addini Da ƙarfafa Tsaro A Nijeriya

Karin Labarai Masu Alaka

Rundunar Sojin Najeriya Ta Dakile Harin ‘Yan Ta’adda A Jihar Borno Labarai
Kasashe Biyar Zasu Tura Sojoji Domin Ayyukan Wanzar Da Zaman Lafiya A Gaza Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
An Kama Maharan Bom Din Maiduguri Tsaro
Amurka Ta Kakaba Takunkumi Ga Kwamandojin Yakin Kasar Sudan Sauran Duniya
Osun: Adeleke Ya Doke Oyebamiji, Ya Ci Gaba Da Rike Kujerar Gwamna Afrika
Gwamnan Gombe Ya kori Wasu Hadimansa Bisa Cin Zarafin Kansila Najeriya

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Sauya Sunan Lafarge Africa Zuwa HBM Nigeria Plc Zai Samar Da Cigaba – Sarkin Fulanin Gombe Afrika
  • Ronaldo Da Messi Ka Iya Hadu A Gasar Cin Kofin Duniya: Ta Ya Ya ? Wasanni
  • ’Yar Kasuwa Ta Tsallake Rijiya Da Baya Bayan Hari Da Saurayinta Ya Kai Mata Afrika
  • Fadar Shugaban Ƙasan Najeriya Ta Musanta Wani Labarin ƙarya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Shugaba Tinubu Ya Tafi Kasar Faransa Afrika
  • Kamfanin Mai Na NNPC Yasamu Gwaggwabar Riba Labarai
  • Rwanda Tana Keta Yarjejeniyar Zaman Lafiya – Tshisekedi Labarai
  • Majalisa Ta Sanya Baki Akan Rikici Tsakanin Dangote Da Hukumar Albarkatun Mai Najeriya
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.