Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Kasar China Ta Sauka Daga Ragamar Bada Bashi
Published: January 27, 2026 at 8:44 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Rawar da China take takawa a zaman wacce take kan gaba wajen bada bashi ga kasashe masu tasowa, ya sauya cikin shekaru 10 da suka wuce, yayin da sabbin basussuka ga kasashe matalauta yake faduwa, yawan kudade da kasashen suke biyan China sun karu sosai, kamar yadda alkaluma daga wata cibiya da ake kira ONE DATA suka nuna.

Chanjin yana zuwa ne a dai dai lokacin da basussuka da kasashe matalauta suke karba daga kungiyoyi da hukumomin kasa da kasa suka karu, da kamar kashi 124 cikin shekaru 10 da suka wuce, wanda yanzu sune ke bada kashi 56 cikin dari na basussuka da kasashen suke karpa daga ketare, da suka kai kimnin dala bilyan 379 da aka bayar tsakanin shekara ta 2020-2024, kididdigar ta nuna.

A bayanai da ake da su na baya bayan nan, daga shekara ta 2020-2024, Afirka taga tasirin mafi girma inda kudade dala bilyan 30 suka shiga baitul mali wasu kasashe dake nahiyar tsakanin shekara 2015-2019, yayin da bilyan 22 ya fita a zaman biyan bashi.

A halin da ake ciki kuma, an fara shari’ar tsohuwar ministan mai ta Najeriya Allison Madueke, ranar Talata, inda masu gabatar da kara suka ce ta karbi cin hanci da rashawa domin bada ayyukan kwangila ta fuskar Makamashi.

A gefe daya kuma, gwamnatin jihar Nija a Najeriya zata yi aiki da Bankin Islama domin habaka samarda makamashi ta rana, kan kudi dala milyan 163, domin kara samarda wutan lantarki da zai taimakawa ayyukan noma da masana’antu, kamar yadda jami’ai suka fada ranar talata.

Labarai

Post navigation

Previous Post: Shugaba Trump Da Gwamnan Minnesota Zasu Sassautawa Bakin Haure
Next Post: Kasar Spain Zata Bada Diyya Ga Iyalen Wadanda Da Suka Rasu A Hatsarin Jirgin Kasa

Karin Labarai Masu Alaka

Kasar Togo Ta Kori Paul Henri Damiba Zuwa Kasar Sa Ta Haihuwa Afrika
Rundunar Hadinkan Saudiya Tayi Ikirarin Mayar Da Martani Ga ‘Yan Aware Labarai
Kasar Ghana Ta Umarci ‘Yan Kasar Su Daina Zuba Jari A Kasashen Waje Afrika
Iran Ta Harbo Jiragen Yakin Amurka Biyu Amurka
Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka Ta Saka Takunkumi Visa Ga Wasu ‘Yan Rwanda Afrika
Ambaliyar Ruwan Sama Yayi Ajalin Mutum 13 A Malawi Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Gwamna Bala Kauran Bauchi Ya Koma Jam’iyar APM Afrika
  • Gwamnatin Najeriya Ta Ayyana Ranakun Hutu Najeriya
  • An Samu Nasarar Karbo Karin Yara 130 Daga Hannun ‘Yan-Ta’adda Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Bayan Shekaru Biyar, Rundunar ‘Yan Sandan Gombe Ta Gano Motar da Aka Sace A Fatakwal Afrika
  • Iran Ta Karyata Tattaunawa Da Washington Afrika
  • Amurka Ta Kai Hari Kan ‘Yan ISISI A Jihar Sakkwato Bisa Rokon Gwamnatin Najeriya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Shugaban Kasar Brazil: Yakamata Amurka Ta Gurfanar Da Shugaban Venezuela A Kotu Afrika
  • Anyi Jana’izar Dan Majalisar Wakilai Yaya Bauchi Tongo Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.