Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Za’a Fuskanci Bala’in Yunwa A Najeriya
Published: November 25, 2025 at 8:38 PM | By: Yusuf Aliyu Harande | Updated: November 25, 2025

Hukumar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta ce hare-haren ‘yan bindiga a yankin Arewacin Najeriya zai haddasa bala’in rashin abinci da ya fi na ko’ina muni a Nahiyar Afirka a cikin shekara mai zuwa.

A wani rahoton da hukumar ta wallafa yau Talata, ta yi kiyasin cewa mutane kimanin miliyan 35 zasu iya fuskantar yunwa a Najeriya a shekara mai zuwa, wanda zai kasance shine mafi muni a duk fadin nahiyar Afirka, kuma mafi muni da za a gani a cikin Najeriya tun daga lokacin da hukumar ta fara tattara irin wadannan alkaluma.

Hukumar ta kuma ce akwai mutane kimanin dubu 15 da zasu fuskanci bala’in mummunar yunwa mai iya kaiwa ga hallaka a Jihar Borno a shekara mai zuwa. Hukumar zata dora jihar Borno a mataki na 5 na bala’in yunwa, wanda shine matakin mafi muni na rashin abinci, kamar irin yadda ake gani a Gaza da Sudan.

Hukumar, wadda ake kira WFP a takaice, ta ce yankin Arewacin Najeeriya zai fuskanci bala’in yunwa mafi muni da bai taba gani ba cikin shekaru 10, inda manoma da mazauna karkara zasu fi shan wahala.

Jami’ain suka ce hare-haren ‘yan bindiga dabam dabam sun hana manoma yin amfani da gonakinsu a Arewa, yayin da a watan Oktoba aka samu wata sabuwar kungiyar ‘yan ta’addar da ita ma ta shiga cikin Najeriya. Wannan kungiya mai suna Jama’at Nusrat al-Islam wal Muslimin, ta saba kai hare-hare a yankin bakin iyakar Nijar, Mali da Burkina Faso.

Labarai, Najeriya

Post navigation

Previous Post: An Kubutar Da ‘Yan Matan Sakandire Su 24 Na Jihar Kebbi
Next Post: Gangamin Wayar Da Kai Don Kawo Karshen Cin Zarafin Jinsi A Jihar Gombe

Karin Labarai Masu Alaka

Tinubu Yace Zayyi Hadaka Da Kasashen Duniya Domin Kawo Karshen Rashin Tsaro. Najeriya
Fiye Da Mutane 10 Sun Mutu A Hatsarin Hanyar Kano Labarai
Iran Tabada Tabbacin Cigaba Da Rufe Mashigar Hormuz Afrika
Najeriya Da Dubai Zasu Karbi Bakoncin Taron Zuba Hannayen Jari Najeriya
Kungiyar Tsaro Ta NATO Tana Fuskantar Kalubale Afrika
Amurka Da Jamhuriyar Dimokraɗiyya Kwango Sun Fara Wata Tattaunawa Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Ministan Sadarwan Kasar Uganda Yayi Allah Wadai Da Kaiwa Bobi Wine Hari Afrika
  • Wasu Yara 50 Sun Kubuta Daga Hannun ‘Yan-Ta’adda Labarai
  • Ga Dukkan Alamu Yaki Tsakanin Rasha Da Ukraine Bai Kare Ba Sauran Duniya
  • Gwamnonin Arewa Sun Yi Jimamin Rasuwar Sarakunan Gumel Da Zurmi Labarai
  • Farashin Mai Ya Tashi A Kasuwannin Duniya Labarai
  • ADC Ta Kaucewa INEC Ta Gudanar Da Babban Taro Labarai
  • Ana Zargin Wani Dan Kasar Libya Da Fataucin Mutane Tsaro
  • An Yaba Wa Gwamnatin Bauchi Bisa Karban Bakuncin Gasar Polo Wasanni
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.