Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

‘Yan Sanda A Tsibirin Bahamas Sun kama Mijin Wata Ba Amurkiya
Published: April 9, 2026 at 9:47 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

‘Yan sanda a tarayyar tsibiran Bahamas sun fada dazu cikin daren nan cewa sun kama mijin wata mata ba Amurkiya wadda ta bace daga wani kwalekwale a kasar.

Hukumomi sun ce an kama mutumin mai shekaru 59 a tsibirin Abaco, ana yi masa tambayoyi. Wani kakakin rundunar tsaron bakin tekun Bahamas ya fadawa kamfanin dillancin labaran AP cewa sun bude bincike game da aikata laifi a wannan lamarin.

‘Yan sandan ba su yi karin bayani ba, haka kuma ba su ce ko an tuhume shi da kisan kai ba.

Jami’ai suka ce matar mai suna Lynette Hooker, ‘yar shekaru 55 da haihuwa, tana tafiya tare da mijin nata a cikin wani kwale kwale mai tsawon kafa 8 daga Hope Town zuwa tsibirin ELbow Cay ranar asabar da daddare, sai mijinta ya fadawa hukumomi cewa ta fada cikin ruwa dauke da makullan jirgin, abinda ya sa sai injin wannan kwale kwale ya daina aiki.

Daga nan ne sai ya fadawa hukumomi cewa yayi amfani da hannunsa wajen ingiza kwalekwalen har zuwa bakin gaba inda ya fada ma wani abinda ya faru da safiyar lahadi.

Amurka, Labarai, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Wani Alkali A Kotun Amurka Ya Dakatar Da Kudurin Shugaba Trump
Next Post: Gwamnatin Tinubu Zata Samar Da Wutan Solar A Jami’ar ADUST Wudil

Karin Labarai Masu Alaka

Gombe Ta Ƙaddamar da Allurar Rigakafin HIV Ta LEN PrEP Afrika
Hukumomin Taliban Sunce A Shirye Suke Domin Sulhu Afrika
Burkina Faso Ta Sako Jami’an Rundunar Sojin Saman Najeriya 11 Da Aka Tsare Tsaro
An Yanke Hukuncin Kisa Ga Hasina Tsohuwar Firaiy-Ministan Bangladash Labarai
Kasar Habasha Ta Cimma Matsaya Da Masu Binta Bashi Afrika
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Rasha: Tura Sojojin Birtaniya Ukraine Zai Kara Ta’azzara Yaki Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Samar Da Tsaro A Jihar Kano Ba Sai An Sa Siyasa Ba! Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Tarayya Tayi Baje Kolin Nasarorin Tinubu Afrika
  • Amurka Ta Cire Takunkumin Da Ta Kakabawa Shugaban Venezuela Amurka
  • Kasashen Amurka Da China Sun Matsawa Ghana Domin Rage Kudaden Haraji Afrika
  • Shirin Safe 0500 UTC Yau Laraba 11.19.2025 Rediyo
  • Janet Ce Gwarzuwar ‘Yar Wasan Mako NWFL Wasanni
  • An Gano Wasu Boma Bomai Da Aka Binne A Jihar Neja Najeriya
  • Zaman Lafiya Yafara Dawowa A Sudan Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.