Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Ministan Yaɗa Labarai Ya Yi Kira Ga Haɗin Kai Domin Bunƙasa Maɗaba’u Afrika
  • Mataimakin Shugaban kasar Najeriya Ya Kaddamar Da Taron Zuba Jari A Jihar Jigawa Afrika
  • Uwargidan Shugaban Ƙasar Najeriya Ta Ƙaddamar Muhimman Ayyuka A Jihar Jigawa Afrika
  • Gwamnatin Najeriya Ta Fara Aikin Babbar Hanyar Da Za Ta Haɗa Jihohin Arewa Afrika
  • Gwamnatin Benue Da MACBAN Sun Kai Ziyarar Ta’aziyya Ga Iyalan Marigayi Ardo Risku Mohammed Afrika

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane A Katsina
Published: May 4, 2026 at 2:03 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Aƙalla mutane goma sha ɗaya sun rasa rayukansu bayan ‘yan bindiga sun kai harin ramuwar gayya a wasu ƙauyuka da ke Ƙaramar Hukumar Kankia a jihar Katsina Najeriya

Majiyoyi rawaito cewa rundunar ƴan sandan jihar ta bayyana cewa harin ya faru ne da misalin ƙarfe 12 na rana a jiya Lahadi, inda maharan suka sake taruwa suka kai farmaki ƙauyukan Jeka da Kolo da Kwalgoro, suka buɗe wuta kan mazauna yankin, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum 11 kafin jami’an tsaro su fatattake su.

Kwamishinan yan sandan jihar, CP Ali Umar Fagge, ya yi Allah-wadai da harin, tare da miƙa ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasu. Ya kuma ba da umarnin a ƙaddamar da farautar masu laifin ta hanyar amfani da bayanan sirri domin cafke su.

Mai magana da yawun rundunar, DSP Abubakar Sadiq, ya ce an ƙara yawan sintiri da aikin share dazuka domin gano maharan da suka tsere, tare da hana aukuwar irin wannan hari a gaba.

Rundunar ta kuma buƙaci al’umma da su kasance masu lura tare da bayar da sahihan bayanai ga jami’an tsaro.

A cewar ‘yan sanda, harin ramuwar gayyar ya biyo bayan nasarorin da jami’an tsaro suka samu a baya-bayan nan, ciki har da dakile satar shanu da kuma kwato dabbobi sama da 200, da kuma fatattakar wasu ‘yan bindiga a wani hari da suka kai.

Hakazalika, gwamnatin jihar Katsina ta yi tir da harin, tana mai cewa hari kan fararen hula aiki ne na ta’addanci. Ta kuma jaddada aniyar ci gaba da haɗin gwiwa tsakanin al’umma da jami’an tsaro domin magance matsalar tsaro.

Afrika, Labarai, Najeriya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: ‘Yan Sanda A Gombe Sun Jaddada Shirin Yaƙi Da Munanan Dabi’u
Next Post: ‘Yan Majalisar Wakilai 17 Sun Fice Daga ADC

Karin Labarai Masu Alaka

Jirgi Marar Matuki Yayi Ajalin A Kallah Mambobin M23 9 Tare Da Kashe Kakakin Rundunar Afrika
Masar Ta Kayyade Farashin Buradi A Kasar Afrika
Masu Goyon Bayan Palasdinawa Sunyi Gangamin Zanga Zanga A Australia Labarai
Hukumar Zaben Najeriya Ta Sanar Da Ranar Zaben Shugaban Kasa Labarai
Zaman Lafiya Yafara Dawowa A Sudan Afrika
Likitoci Masu Neman Kwarewa Zasu Shiga Yakin Aiki Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Ministan Yaɗa Labarai Ya Yi Kira Ga Haɗin Kai Domin Bunƙasa Maɗaba’u
  • Mataimakin Shugaban kasar Najeriya Ya Kaddamar Da Taron Zuba Jari A Jihar Jigawa
  • Uwargidan Shugaban Ƙasar Najeriya Ta Ƙaddamar Muhimman Ayyuka A Jihar Jigawa
  • Gwamnatin Najeriya Ta Fara Aikin Babbar Hanyar Da Za Ta Haɗa Jihohin Arewa
  • Gwamnatin Benue Da MACBAN Sun Kai Ziyarar Ta’aziyya Ga Iyalan Marigayi Ardo Risku Mohammed

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Majalisar Dattawa Ta Wanke Janar Christopher Musa A Matsayin Minista Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Amurka Ta Girke Jirage Marasa Matuki Tare Da Sojoji A Najeriya Afrika
  • Kayan Jinya Da Ayyukan Kiwon Lafiya Suna Barazanar Karewa A Sudan Kiwon Lafiya
  • Shirin Safe 0500 UTC Yau Litinin 11.17.2025 Rediyo
  • An Tsinci Gawar Yarinya A Gombe Najeriya
  • Sojin Najeriya Da ‘Yan Ta’adda Sunyi Taho Mugama Najeriya
  • Gwamnatin Najeriya Taja Hankalin ‘Yan Najeriya Mazauna Iran Da Kasashen Larabawa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gasar Cin Kofin Nahiyar Afrika A Wannan Makon Wasanni
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.