Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Sanata Goje: Sakamakon Zaben Daga Abuja Zai Fito
Published: May 19, 2026 at 10:30 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Sanata Muhammadu Danjuma Goje yayi watsi da samakon zaben dake yawo inda yace bashida tushe, mara inganci ne.

Tsohon Gwamnan jihar Gombe kuma Sanata Mai ci Karo na hudu Danjuma Goje yace sakamakon zaben dake yawo bashida tushe balle madafa.

Goje dai shine Sanata mai wakiltar mazabar Gombe ta tsakiya a majalisar dattawan Najeriya, Wanda yake kan kujerar tun 2011.

A yayin da yake jawabi a madadin Sanatan Goje hadimin sa Alhaji Ahmed Isa Kashere, yace sakamakon zaben fidda gwani na yankin Akko da Yamaltu Deba da akayi a ranar Litinin basu kammala ba kuma ba’a sanar ba!

A yayin da ya zargi wasu gidajen jaridu da sabbin kafafen sada zumunta da yada labarin karya mara inganci.

Sanata Danjuma Goje yayi kira ga magoya bayan sa da yan jam’iyar da al’ummar mazabar sa dasu kwantar da hankalin su kuma suyi watsi da sakamakon zaben dake yawo bashida tushe kuma mara inganci.

Ya kara da cewa “A madadin Sanata Danjuma Goje ina shawartan al’ummar mazabar Gombe ta tsakiya wanda suka hada da kananan hukumomin Akko da Yamaltu Deba suyi watsi da wannan labarin kanzon kurege dake yawo daga makiya jam’iyar muta APC me daraja.

Bari mu kawar muku da shakku, muna masu tabbatar muku cewa har yanzu sakamakon zaben fidda gwani ba’a baiyana ba tukun na, saboda kamar yadda uwar jam’iya ta kasa ta tsara sakamakon zaben za’a fade sane a ofishin jam’iyar APC na Kasa dake Abuja.

Ya sake kira da masoya da magoya baya da al’umma baki daya da su kara hakuri sujira sanarwan sakamakon zaben a hukumance.

A matsayin sa na dattijo kuma mai gabatar da doka da oda, mai fada aji a jihar Gombe ya tsaya ne akan ra’ayin sa na bin ka’idodi da tsari sannan da kiyaye dokokin da jam’iyar APC ta gindiya

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Jarman Deba Ya Kada Senata Goje A Zaben Fidda Gwani
Next Post: NYSC – Sai An Gabatar Da Takardar NERD Kafin Shiga Bautar Ƙasa

Karin Labarai Masu Alaka

Gidauniyar Sultan Ta Jaddada Muhimmancin Kula Da Lafiyar Yara A Gombe Afrika
Ganduje Ya Nisanta Kansa Da Batan Dadiyata Labarai
Majalisar Wakilai Ta Rikon Kwaryar Nijar Ta Gudanar Da Zama Karo Na Biyu Afrika
Iran Ta Kai Hari Matatar Mai A Kuwait Afrika
Iran Da Amurka Sun Gindayawa Juna Ka’idojin Tsagaita Wuta Afrika
Gwamnatin Kano: Zamu Kara Daukar Malamai Domin Inganta Ilimi Najeriya

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Yobe Ta Sake Jaddada Ƙudirin Rage Mutuwar Yara Afrika
  • Kamaru Ta Lallasa Malawi 3-0, Ta Lashe Kofin WAFCON Na Farko A Tarihi Wasanni
  • An Zargi Babban Mai Gabatar Da Kara A Kotun Duniya Ta ICC Afrika
  • Bayan Rikicin Manoma Da Makiyaya, Kwamitin White Paper Ya Ziyarci Bojude Da Kwami Afrika
  • Kasar Iceland Ta Kauracewa Bikin Gasar Wakokin Shekara Mai Zuwa Labarai
  • Trump Yace Kawayen Amurka A Kungiyar NATO Basa Goyon Bayan Su Afrika
  • An Katse Intanet Da Wayar Tarho A Kasar Uganda Siyasa
  • Gwamna Abba Ya Gana Da Kwankwaso Kamun Ganawarsa Da Tinubu Siyasa
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.