Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Gidauniyar Sultan Ta Jaddada Muhimmancin Kula Da Lafiyar Yara A Gombe
Published: September 3, 2026 at 4:29 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Masarautar Kaltungo a jihar Gombe dake arewa maso Gabashin Najeriya ta karɓi baƙuncin wani taron yini ɗaya na daidaita ayyukan kiwon lafiya, wanda Gidauniyar Sultan Foundation for Peace and Development ta shirya tare da haɗin gwiwar Hukumar Bunƙasa Kula da Lafiya Matakin Farko ta jihar Gombe.

Taron, wanda ya haɗa sabbin jami’an da aka ɗauka daga masarautu da ƙananan hukumomi tare da sauran masu ruwa da tsaki, ya mayar da hankali ne kan ƙarfafa haɗin gwiwa da ƙara shigar al’umma wajen aiwatar da shirye-shiryen kiwon lafiya, musamman na yara da mata.

Da yake buɗe taron, Mai Kaltungo, Injiniya Saleh Muhammad, ya buƙaci mahalarta su kasance masu kyautatawa, sauraro da kuma mai da hankali, tare da nuna jajircewa wajen ganin an cimma manufofin shirin.

Mai martaban ya kuma waiwayi tarihin yadda sarakunan gargajiya suka taka muhimmiyar rawa a harkokin kiwon lafiya a Najeriya, yana mai cewa masarautun gargajiya na da muhimmiyar gudunmawa wajen wayar da kan jama’a da tallafa wa shirye-shiryen gwamnati na inganta kiwon lafiya.

A nasa ɓangaren, Babban Jami’in Ayyuka na Sultan Foundation, Barrister Haruna Yusuf, ya jaddada muhimmancin kula da yara da samar musu da abinci mai gina jiki domin inganta lafiyarsu da bunƙasa rayuwarsu.

Barrister Yusuf ya kuma yaba da ƙoƙarin sarakunan gargajiya, ƙarƙashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi, bisa gudunmawar da suke bayarwa wajen inganta lafiyar yara, iyaye mata da sauran al’umma.

Shi ma Dr. Kassim Muhammad ya jaddada muhimmancin allurar rigakafi wajen kare al’umma daga cututtuka, tare da bayyana muhimmiyar rawar da sabbin jami’an da aka ɗauka za su taka wajen sa ido da tabbatar da dorewar ayyukan rigakafi a faɗin Jihar Gombe.

Ya yi kira da a ƙara wayar da kan jama’a domin su fahimci cewa allurar rigakafi ba ta da illa, yana mai cewa rashin yi wa yara rigakafi a lokacin ƙuruciya na iya haifar da matsaloli ga lafiyarsu a nan gaba.

Taron ya kuma samu halartar masu ruwa da tsaki, inda mahalarta suka gabatar da tambayoyi tare da samun amsoshi da ƙarin haske daga masu jawabi kan batutuwan da suka shafi rigakafi, abinci mai gina jiki da sauran muhimman harkokin kiwon lafiya.

Afrika, Kiwon Lafiya, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Nishadi, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: FIFA Ta Ba Da Goyon Bayanta Ga Gyaran Ƙwallon Ƙafa A Najeriya, Shehu Dikko Ya Gana Da Infantino
Next Post: Gwamnonin Arewa Sun Yi Jimamin Rasuwar Sarakunan Gumel Da Zurmi

Karin Labarai Masu Alaka

Shugaban Amurka Donald Trump Yace Amurka Zata Kai Babban Farmaki Iran Afrika
Wakilan Majalisar Dokokin Phillipines Suna Yunkurin Tsige Shugaban Kasar Afrika
Ansamu Maganin Da Yake Rage Kitsen Jijiyoyi A Amurka Amurka
An Kaiwa Sojojin Ghana Hari Da Makami Mai Linzami Afrika
NUJ Gombe Ta Ƙarfafa Bin Ɗa’a A Aikin Jarida, Ta Kaddamar Da Kwamitin Ladabtarwa Afrika
Gwamnan Bauchi Ya Shiga Neman Mafita Kan Lalacewar Matatar Ruwan Alkaleri Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Sallah Sai Ranar Juma’a A Najeriya: Fadar Sarkin Musulmi Afrika
  • Masoya Kungiyar Kwallon Kafar Morocco Suna Cikin Farin Ciki Bisa Hukuncin Kotu Afrika
  • Tattalin Arzikin Najeriya Ya Karu A Karshen 2024 Rediyo
  • Wani Alkali A Kotun Amurka Ya Dakatar Da Kudurin Shugaba Trump Afrika
  • Tattaunawar Nukiliya Tsakanin Iran Da Amurka Yana Tasirin Akan Farashin Albarkatun Mai Amurka
  • Jam’iyyar ADC Ta Karbi Peter Obi Da Wasu Manyan ‘Yan-Siyasa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Jami’an Shiga Da Fice A Afirka Ta Kudu Sun Tafka Badakalar Kudade Afrika
  • Aisha Buhari Ta Bayyana Irin Kalubalen Da Ta Fiskanta Sakamakon Biyewa Jita-Jita Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.