Ma’aikatan Babban Bankin Najeriya (CBN), reshen Gombe, sun gyara Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin farko da ke Wajari, a Ƙaramar Hukumar Yamaltu Deba ta jihar Gombe, a matsayin wani ɓangare na shirin tallafa wa al’umma na kamfanin, wato CSR.
A cewar wata sanarwa da Jami’in Yaɗa Labarai na Ƙaramar Hukumar Yamaltu Deba, Comrade Babangida Umar Deba, ya sanya wa hannu, an ƙaddamar da cibiyar kiwon lafiyar da aka gyara a wani biki da ya samu halartar shugabannin al’umma, wakilan gwamnati da jami’an Babban Bankin Najeriya..

Da yake jawabi a wajen bikin, Mataimakin Shugaban Ƙaramar Hukumar Yamaltu-Deba, Alhaji Mohammed D. Jalo, wanda ya wakilci Shugaban Ƙaramar Hukumar, Alhaji Yunusa Yakubu, ya yaba wa ma’aikatan CBN bisa zaɓar Wajari domin aiwatar da wannan aikin.
Ya bayyana wannan mataki a matsayin wata alama ta tausayi da kuma ƙudurin inganta jin daɗi da walwalar al’ummomin da ke karɓar ayyukan ma’aikatan, tare da gode musu da addu’ar Allah Ya saka musu da alheri.
Shi ma ɗan majalisar dokokin jihar Gombe mai wakiltar mazabar Deba, Alhaji Mohammed Kabiru Kuri, ya yi kira ga al’ummar Wajari da su ɗauki cibiyar a matsayin tasu, tare da tabbatar da cewa an kula da ita yadda ya kamata domin amfanin al’ummar yanzu da kuma na ƙarni masu zuwa.
A nasa jawabin, Hakimin Wajari kuma Wamban Deba, ya bayyana godiya ga ma’aikatan CBN bisa wannan tallafi, yana mai cewa gyaran cibiyar babbar gudummawa ce ga lafiyar al’umma da jin daɗinsu.
Ya kuma yi kira da a ƙara kai irin waɗannan ayyukan ci gaba zuwa Wajari da sauran al’ummomin da ke makwabtaka da yankin.
A wata Tattaunawa da Kansilan Gundumar Wajari, Malam Musa Hassan Wajari, ya ce an lalata tare da wawushe cibiyar kiwon lafiyar tsawon shekaru, ba tare da samun kulawar da ta dace ba, duk da kai rahotanni ga hukumomin da abin ya shafa.
Ya ce shiga tsakani da ma’aikatan CBN suka yi ne ya taimaka wajen dawo da cibiyar cikin yanayin da za ta iya ci gaba da gudanar da ayyukanta, inda ya buƙaci mazauna yankin su sanya ido tare da kare cibiyar daga sake fuskantar ɓarna.
Da yake magana kan wannan shiri, Shugaban Reshen CBN na Gombe, Alhaji Yunusa Buba Mubi, ya bayyana cewa gyaran cibiyar na daga cikin al’adun ma’aikatan CBN na bayar da gudummawa daga cikin abin da suke samu domin tallafa wa al’ummomin da suke gudanar da ayyukansu a cikinsu.
A cewarsa, wannan mataki wata hanya ce ta nuna godiya ga al’ummomin da ke samar da zaman lafiya da yanayi mai kyau da ke ba ma’aikatan CBN damar gudanar da ayyukansu cikin kwanciyar hankali.
Ya yi kira ga al’ummar Wajari da su ɗauki cibiyar a matsayin tasu, su tabbatar da kula da ita yadda ya kamata, tare da yin amfani da ayyukan kiwon lafiyar da ake bayarwa a cikinta.
Bikin ya ƙare da nuna godiya daga al’ummar Wajari ga ma’aikatan CBN bisa wannan gagarumar gudummawa, tare da addu’ar Allah Ya ci gaba da ba su nasara da albarka, da kuma duk waɗanda suka bayar da gudummawa wajen gyaran cibiyar kiwon lafiyar.


