Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Filato: Gwamnati Ta Ƙarfafa Matakan Kariya Yayin Sake Buɗe Makarantu
Published: September 12, 2026 at 11:17 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnatin jihar Filato a Najeriya ta bayar da umarnin bude dukkan makarantun firamare da sakandare na gwamnati da masu zaman kansu a jihar daga ranar Litinin 14 ga Satumba, 2026.

Kwamishiniyar yada labarai da sadarwa, Joyce Lohya Ramnap, ce ta sanar da hakan a cikin wata sanarwa a ranar Juma’a, inda ta ce matakin ya biyo bayan matakan riga-kafi da aka dauka domin dakile yaduwar cutar diphtheria wato Mashako wanda ya hallaka yara da dama sassan jihar, yayinda wassu ke jinya a cibiyoyin lafiya a jihar.

Dakta Job Maren, shine shugaban sashen dake kula da cututtuka masu yaduwa a jihar Filato, yace sun lura cewa mafi yawan wadanda suka kamu sa cutar basu yi rigakafi ba.

A makon jiya ne gwamnatin jihar ta Filato ta sanar da rufe makarantu na wani dan lokaci don baiwa hukumomin lafiya damar karfafa ayyukan sa ido kan bullar Diphtheria a wassu kananan hukumomin jihar.

Malam Bala Kwamanda dake garin Bukur a karamar hukumar Jos ta Kudu a jihar Filato ya bukaci iyaye su dau matakan kariya a gida da kuma kan yaransu dake zuwa makarantu.

Gwamnati ta umurci hukumomin makarantu da su kula da tsaftar muhalli da tsaftar dalibai tare da sanya ido sosai don gano alamomin cutar, don samun kulawar gaggawa.

Gwamnati ta kuma shawarci jama’a game da rashin fa’idar yin amfani da magungunan ba’a tantance sahihancinsu ba ko kuma boye wadanda ke da alamun cutar, tana mai jaddada cewa ganowa da kuma magance cutar da wuri na da matukar muhimmanci wajen hana ci gaba da yaduwar curar a tsakanin al’umma.

Ga rahoton Wakiliyar GTA Hausa Amurka Ke Magana a jihar Filato Zainab Babaji

https://gtahausa.com/wp-content/uploads/2026/09/AUD-20260912-WA0020.mp3
Afrika, Kiwon Lafiya, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi

Karin Labarai Masu Alaka

Karo Na Biyu Cikin Kwanaki 29 An Samu Gobara A Kasuwar Katako Labarai
An Yanke Mishi Hukuncin Kisa Saboda Neman Kudin Aure Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Eziekel Gomos Ya Zamo Babban Daraktan Sakatariyar Zauren Gwamnonin Arewa Najeriya
Amurka Ta Kulla Yarjejeniya Da Kasashe Hudu Domin Inganta Kiwon Lafiya Labarai
‘Yan Sanda A Jihar Gombe Sun Karyata Kona Gidan Nafiu Bala Afrika
Rundunar ‘Yan Sanda Ta Bukaci Al’umma Su Kiyaye Doka Yayin Bikin Takutaha Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Filato: Gwamnati Ta Ƙarfafa Matakan Kariya Yayin Sake Buɗe Makarantu
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Trump: Isra’ila Ta Daina Kai Hari Ga Duk Cibiyar Iskar Gas Afrika
  • Kamaru Ta Lallasa Malawi 3-0, Ta Lashe Kofin WAFCON Na Farko A Tarihi Wasanni
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Dan Takarar Gwamna Na Jam’iyyar APM A Bauchi Ya Bada Gudummawar Naira Miliyan ₦21 Ga Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Bara Da Shira Labarai
  • Majalisar Tarayya Ta Amince Da Gyara Dokar Kasafin Kudi Labarai
  • Jami’an Shige Da Ficen Amurka Sun Harbe Wani Har Lahira Amurka
  • ‘Yan Majalisar Wakilai 17 Sun Fice Daga ADC Afrika
  • Shugaban Hukumar NAHCON Ya Ajeye Mukaminsa Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.