Kwamishinan ’Yan Sandan jihar Gombe, CP Umar Ahmed Chuso ya karɓi sabon Kwamandan Hukumar Tsaron (NSCDC) na jihar Gombe, CC Mohammad Usman Inuwa, mni, wanda ya kai masa ziyarar girmamawa.
Taron ya ba da damar ƙarfafa haɗin gwiwa da kyakkyawar alaƙa tsakanin hukumomin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya, kiyaye doka da oda a faɗin Jihar Gombe.
A yayin ziyarar, CP Umar Ahmed Chuso ya jaddada muhimmancin ingantaccen haɗin gwiwa, musayar bayanan sirri da kuma gudanar da ayyukan tsaro cikin haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro, domin tunkarar ƙalubalen tsaro da kuma dorewar zaman lafiyar da ake samu a jihar.
Ya kuma bayyana shirye-shiryen rundunar ’yan sandan na yin aiki kafada da kafada da NSCDC da sauran hukumomin tsaro da abin ya shafa, domin inganta tsaron al’umma da tabbatar da samar da muhalli mai aminci ga mazauna Jihar Gombe.
A nasa martanin, CC Mohammad Usman Inuwa, mni, ya bayyana aniyarsa ta ƙarfafa kyakkyawar alaƙar aiki da rundunar ’yan sanda da sauran masu ruwa da tsaki a harkokin tsaro, domin haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen yaƙi da barazanar tsaro.
Taron ya sake jaddada aniyar rundunar ’yan sandan Najeriya da Hukumar Tsaro ta Farar Hula ta Ƙasa (NSCDC) na ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro, domin cimma muradun zaman lafiya, tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a Jihar Gombe.


