Wani mummunan hatsarin mota ya yi sanadin mutuwar yara biyar daga iyali ɗaya a jihar Gombe dake arewa maso Gabashin Najeriya bayan wani keke Napep da ke ɗauke da su zuwa makaranta ya yi karo da tankar ruwa.
Yaran da suka mutu duk ’ya’yan gidan Mansir Adamu ne, kuma suna karatu a makarantu daban-daban a cikin garin Gombe.
An bayyana sunayen yaran da suka rasu da Maryam Mansir Adamu da Usman Mansir Adamu, waɗanda dukkansu ɗaliban aji biyar ne a makarantar firamare ta Jekadafari.
Sauran yaran su ne Hauwau Mansir Adamu, ɗalibar makarantar sakandaren ƙaramar hukumar Jekadafari (GJSS Jekadafari), da Aliyu Mansir Adamu, ɗalibin makarantar sakandaren gwamnati ta Ahmadu Gombe (GDSS Ahmadu Gombe), da kuma Fatima Mansir Adamu, wadda ita ma ɗaliba ce.
Hatsarin ya jefa iyalan yaran cikin alhini, tare da girgiza al’ummar Jekadafari da kuma makarantun da yaran suke karatu.


