Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Gurbin Yaya Tongo: INEC Ta Tsayar Da 19 Ga Satumba Don Zaɓen Cike Gurbi
Published: August 19, 2026 at 1:03 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta a Najeriya wato (INEC) ta tsayar da Asabar, 19 ga Satumba, 2026 a matsayin ranar da za a gudanar da zaɓen cike gurbin kujerar wakiltar Gombe/Kwami/Funakaye a Majalisar Wakilan Tarayya.

Za a gudanar da zaɓen ne domin cike gurbin da ya samu sakamakon rasuwar ɗan majalisar da ke wakiltar mazabar, Honarabul Yaya Bauchi Tongo, wanda ya rasu yana da shekaru 62 bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

INEC ta bayyana cewa za a gudanar da zaɓen ne bisa tanadin Sashe na 76(2) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999, kamar yadda aka yi wa gyara, da kuma sauran tanade-tanaden dokar zaɓe.

A cikin jadawalin da hukumar ta fitar, za a wallafa Sanarwar Zaɓe a ranar Alhamis, 20 ga Agusta, 2026.

Hukumar ta kuma tsara cewa jam’iyyun siyasar da ke da niyyar tsayar da ’yan takara su gudanar da zaɓen fidda gwani tsakanin 21 zuwa 25 ga Agusta, 2026.

Bayan kammala zaɓen fidda gwani da sauran matakan tantance ‘yan takara, INEC za ta wallafa jerin sunayen ’yan takarar da aka amince da su a ranar 8 ga Satumba, 2026.

A cewar jadawalin, yakin neman zaɓe na hukuma zai fara ne a 9 ga Satumba, sannan ya ƙare a 17 ga Satumba, 2026, kwanaki biyu kafin ranar zaɓen.

Mazabar Gombe/Kwami/Funakaye ta ƙunshi Kananan Hukumomi uku, wato Gombe, Kwami da Funakaye. INEC ta ce za a gudanar da zaɓen a faɗin rumfunan zaɓe 903 da yankunan rajista 31 na mazabar.

Hukumar ta yi kira ga dukkan jam’iyyun siyasa da ’yan takararsu da su bi jadawalin da aka tsara tare da gudanar da dukkan harkokinsu cikin bin dokokin zaɓe.

INEC ta kuma tabbatar wa masu ruwa da tsaki a mazabar cewa tana da cikakken shiri na gudanar da zaɓe cikin ’yanci, adalci da gaskiya, tare da samar da dama iri ɗaya ga dukkan jam’iyyun siyasa da ’yan takara.

Hukumar ta kuma yi kira ga masu kada kuri’a da su fito su gudanar da haƙƙinsu na ɗan ƙasa cikin lumana da sanin ya kamata.

Zaɓen na ranar 19 ga Satumba, 2026 na daga cikin zaɓukan cike guraben kujerun majalisun dokokin da INEC ta tsara gudanarwa a wasu jihohin Najeriya.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Shirye-Shirye, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Manchester United Na Dab Da Kammala Daukar Carlos Baleba Daga Brighton
Next Post: Kuɗaɗen Da EFCC Ta Kwato Za Su Tallafa Wa Shirin Lamunin Karatu

Karin Labarai Masu Alaka

Gwamnan Neja Bago Na Cin Zarafin Talakawan Da Suka Zabe Shi Labarai
AIG Kwaimo Ya Kai Ziyarar Aiki Gombe, Ya Buƙaci Ƙara Ƙaimi A Yaƙi Da Ta’addanci Labarai
Amurka Ta Baiwa Najeriya Wasu Muhimman Kayan Yaki Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Guterres: Babban Kuskure Ne Yadda Isra’ila Ta Kai Farmaki A Gaza Labarai
An Kashe Mutane 25 Yayin Kai Wasu Hare Hare Jihar Adamawa Labarai
Kamfanin Dangote Zai Sayo Na’urori Daga Kasar China Kimiya

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Na Yi Murabus Ne Don Amurka Ta Keta Haddin Iraniyawa Amurka
  • An Kashe Falatsinawa Biyar A Wani Hari Da Isra’ila Takai Wata Makaranta A Gaza Tsaro
  • Jami’an tsaro sama da dubu biyar ne zasuyi aikin tabbatar da tsaro Alokacin bikin karamar sallah a Jihar Nejan Najeriya. Najeriya
  • Bayan Rikicin Manoma Da Makiyaya, Kwamitin White Paper Ya Ziyarci Bojude Da Kwami Afrika
  • Gobara Ta Tashi A Makarantar Koyon Jinyar Dabbobi Dake Jihar Kano Najeriya
  • Farashin Mai Ya Tashi A Kasuwannin Duniya Labarai
  • Suvr Jahun: Ya Kamata Obasanjo Ya Bar Al’umar Ƙasa Su Fito Da Wadda Suke So 2027 Najeriya
  • Abun Da Kuke Buƙatar Sani Game Da Gasar Cin Kofin Ƙasashen Afirka 2025 Wasanni
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.