Shugaban Ƙasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin karkatar da kuɗaɗen da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta kwato zuwa Asusun Bayar da Lamunin Karatu na Nijeriya (NELFUND), domin ƙara ƙarfafa shirin bayar da lamunin karatu ga ɗaliban manyan makarantu a ƙasar.
Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin da yake yi wa manema labarai bayani a Fadar Shugaban Ƙasa, bayan kammala taron Majalisar Zartarwa ta Ƙasa (FEC).
A cewar ministan, Majalisar ta kuma amince da karkatar da wasu kuɗaɗen da ba a karɓa ba, ciki har da kuɗaɗen riba da ba a karɓa ba da ke cikin Capital Market Trust Fund da Dormant Account Trust Fund, zuwa shirin lamunin karatu.
Dr. Alausa ya ce matakin na daga cikin ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya na tabbatar da samar da isassun kuɗaɗe da za su bai wa NELFUND damar faɗaɗa shirin, tare da tabbatar da cewa ɗaliban da ke buƙatar tallafin kuɗi sun samu damar ci gaba da karatunsu.
Ya ƙara da cewa amfani da waɗannan kuɗaɗe zai taimaka wajen tabbatar da ɗorewar tsarin bayar da lamunin karatu, tare da rage matsalolin kuɗi da ka iya hana wasu ɗalibai ci gaba da karatu a manyan makarantu.
Gwamnatin Tarayya ta kafa NELFUND ne domin samar da tallafin kuɗi ga ɗaliban manyan makarantu, musamman waɗanda ke fuskantar matsalar biyan kuɗaɗen karatu.
Sabon matakin na zuwa ne yayin da Gwamnatin Tarayya ke ci gaba da faɗaɗa shirin lamunin karatu, da nufin ƙara yawan ɗaliban da za su iya cin gajiyarsa a faɗin Nijeriya.


