Kotun jihar Gombe ta ɗauki hayar kamfanin ba da shawara domin horas da lauyoyi da masu gudanar da cibiyoyin kasuwanci kan yadda ake yin rajistar takardun rantsuwa ta intanet, a wani yunƙuri na shigar da tsarin rijistar takardun rantsuwa na zamani a jihar.
An gudanar da horon ne a harabar babbar kotun jihar Gombe da ke kan hanyar Gombe Bypass, inda aka haɗa lauyoyi da masu gudanar da cibiyoyin kasuwanci domin wayar musu da kai kan yadda za su yi amfani da sabon tsarin rajistar takardun rantsuwa ta yanar gizo.
Da yake zantawa da manema labarai yayin horon, babban mai ba da shawara na kamfanin Century Communication System Limited, Mista Solomon Adetunbi, ya ce shirin wani ɓangare ne na ƙoƙarin faɗaɗa amfani da fasahar zamani wajen gudanar da ayyukan kotuna, bayan fara amfani da tsarin kotunan lantarki kimanin shekaru uku da suka gabata.
Ya bayyana cewa sabon tsarin zai ba mazauna jihar damar neman takardun rantsuwa daga duk inda suke, ba tare da sun je kotu da kansu ba.
A cewarsa, wannan tsari zai sauƙaƙa wa jama’a samun takardun rantsuwa, musamman waɗanda ke zaune a yankunan karkara da ke da nisa da kotuna.
Mista Adetunbi ya kuma bayyana cewa za a buɗe shafin yanar gizon domin rajistar wakilai daga mako mai zuwa, inda masu sha’awar shiga tsarin za su samu damar yin rajista.
Wasu daga cikin mahalarta horon, ciki har da Sakatariyar ƙungiyar lauyoyi ta Najeriya (NBA), reshen jihar Gombe, Barrister Kuburat, da wakilan kamfanin Cimark Multi Vics da ke Tunfure, sun bayyana cewa sabon tsarin zai inganta ayyukan hidima ta hanyar rage jinkiri da sauƙaƙa rajistar takardun rantsuwa.
Sun ce amfani da fasahar zamani wajen yin rajistar zai taimaka wajen rage wahalhalun da masu buƙatar takardun rantsuwa ke fuskanta, tare da samar da hanya mafi sauri da sauƙi ta samun wannan sabis.
Mahalarta horon sun kuma yaba wa kamfanin Century Communication System Limited bisa shirya shirin wayar da kai, inda suka bayyana shi a matsayin wani muhimmin mataki na inganta ayyukan shari’a da sauƙaƙa wa jama’a samun hidimomin kotu.


