Shari’ar Sirika: Mai Binciken Efcc Ya Sha Tambayoyi Kan Zargin Ba Da Kwangilar Madakatar Jirgi A Katsina
Mai binciken hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC Mr.Christopher Odofin ya ce bai an san samu takaddama tsakanin rundunar sojan sama, hukumar filayen jiragen sama ko gwamnatin Katsina kan bigiren aikin gina madakatar jirgi a filin saukar jiragen sama na Katsina ba.
Wannan ya zo ne a cigaba da shari’ar tsohon ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika gaban babbar kotun birnin tarayya a Maitama Abuja.

Lauyan kamfanin Al-Buraq da EFCC ta ke zargi an damkawa kwangilar M.J Numa San ya jefa tambayoyi ga Mr.Odofin har ya kai ga lauyoyi sun yi dariya ga irin amsoshin da Odofin ke bayarwa na nuna bai yi binciken kwakwaf gabanin gabatar da shaidar ta sa ta zargin samun zarmiya ba.
MJ.Numa ya tambayi Odofin ko akwai sa hannu da tilasta umurni a kwangilar amma Odofin ya ce babu.

Wata tambayar da Odofin ya ce bai sani ba ita ce takaddama da ta kawo tsaiko ga kamfanin Al-Buraq wajen aiwatar da kwangilar kuma Odofin bai fadada binciken ba zuwa jin ta bakin rundunar sojan sama, hukumar kula da filayen jirgi ko ma’aikatar filaye ta jihar Katsina kan takaddamar filin aikin kwangilar.
Kazalika duk bayanan sun nuna mai hakkin sanya hannu kan kwangilolin shi ne tsohon babban sakataren ma’aikatar sufurin jirgaen Mr. Abel Olumuyiwa Enitan wanda a yanzu shi ne shugaban ma’aikata na tarayya.
Hakanan Mr.Odofin bai musanta aikin gyare-gyare na filin saukar jiragen sama na Katsina ya samu amincewar hukumar ba da damar kwangiloli ga kamfabnoni ba wato BPE.
Alkalin kotun Jostis Sylvanus Oriji wanda har ya shigo ya ce ba laifi ba ne tantance hujjoji daga lauyan kariya yayin da babban lauyan EFCC Rotimi Jacobs ya nuna damuwa tambayoyin kurel na MJ.Numa, ya dage cigaba da bahasi zuwa ranar 19 ga watan nan na Nuwamba da 15 ga watan Disamba.

