Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana shirin gwamnatin sa na siyo jirage marasa matuka da kayan aikin sa’ido da saurin mayar da martani domin kare mazauna iyakokin Kano da Katsina daga hareharen ’yan ta’adda
Wannan ya zo ne yayin da gwamnan ke duba shirin Joint Task Force (JTF) wajen tunkarar hareharen kwanan nan a kananan hukumomin tsanyawa da Shanono, inda aka sace mutane kimanin 5 a tsanyawa da 10 a Shanono, ciki har da mace guda da ta rasa rayuwarta.
Gwamna ya roki mazauna yankunan da su ba da bayanai masu amfani kan motsin ’yan bindiga, sannan ya umarci JTF da su yi iyakar ƙoƙarinsu wajen kubutar da wadanda aka sace.
Ya tabbatar wa dakarun da iyalan da abin ya shafa cewa gwamnati na yin iyakar ƙoƙarin ta wajen mayar da wadanda aka sace ga iyalansu cikin kankanin lokaci.


