Duk abin da kuke buƙatar sani game da Gasar Cin Kofin kasashen Afirka ta 2025.
Manyan ‘yan wasan ƙwallon ƙafa na Afirka za su nufi Morocco yayin da Gasar Cin Kofin Afirka ta 2025 ta zama gasa ta farko da aka shirya a lokacin Kirsimeti da Sabuwar Shekara.
Masu masaukin baki za su buɗe gasar a ranar Lahadi, 21 ga Disamba, inda za su fafata da Comoros a filin wasa na Prince Moulay Abdellah da ke Rabat da ƙarfe 19:00 GMT.
A jaddawalin Fifa Morocco tana matsayi na 11 a duniya rabon ta ɗaga kofin tun 1976, wannan shine wasa karo na 35.
Ga yadda aka tsara ƙungiyoyin

Ƙungiyoyin Kwallon Kafa na Ƙasashe ashirin da huɗu (24) za su fafata bisa tsarin rukuni shida (6) a kowani rukuni a kwai huɗu, inda ƙungiyoyi biyu a kowace rukuni tare da ƙungiyoyi huɗu mafi kyau da suka zo na uku za su kai zagaye na 16.

Rukunin A:
Morocco, Mali, Zambia, Comoros
Rukunin B:
Masar, Afirka ta Kudu, Angola, Zimbabwe
Rukunin C:
Najeriya, Tunisia, Uganda, Tanzania
Rukunin D:
Senegal, DR Congo, Benin, Botswana
Rukunin E:
Algeria, Burkina Faso, Equatorial Guinea, Sudan
Rukunin F:
Ivory Coast, Kamaru, Gabon, Mozambique
Gasar Afcon 2025 Za Ta Fara Ne Kamar Haka:
Wasan farko zai fara da ƙarfe 19:00 GMT a ranar 21 ga Disamba, har zuwa 31 ga Disamba, inda za’a keb buga wasanni huɗu a kowace rana da ƙarfe 12:30 GMT, 15:00 GMT, 17:30 GMT da kuma 20:00 GMT
Wasannin zagayen rukuni na ƙarshe za su fara ne da ƙarfe 16:00 ko 19:00 GMT.
Matakin kihuwa daya kuma (Knockout) zai fara ne a ranar Asabar, 3 ga Janairu, zuwa ranar Lahadi, 18 ga Janairu da ƙarfe 19:00 GMT.
Filayen Da Za’a Buga Wasanni:
Morocco ta gyara filayen wasa a duk faɗin ƙasar don shirye-shiryen gasar AFCON 2025 yayin da take kokarin ganin ta dauki matsayin mai masaukin baki na gasar cin kofin duniya a 2030.
Filaye tara dake fadin birane shida a ƙasar ta Morocco za su karbi bakuncin wasannin, ciki har da guda hudu a Rabat:
Rabat
• Filin wasa na Prince Moulay Abdellah mai daukan mutum (69,500)

Filin wasa na Complexe Sportif Prince Moulay Abdellah Olympic mai daukar mutum (21,000)
• Complexe Sportif Prince Heritier Moulay El Hassan mai daukar mutum (22,000)
• Stade El Barid mai daukar mutum (18,000)
• Grande Stade d’Agadir, Agadir mai daukar mutum (45,480)
• Complexe Sportif de Fes, Fes mai daukar mutum (45,000)
• Grande Stade de Marrakech, Marrakech mai daukar mutum (45,240)
• Stade Mohammed V, Casablanca mai daukar (67,000)
• Grande Stade de Tangier, Tangier mai daukar mutum (68,000)
Inda za’a buga wasan karshe a Rabat.

Cikakken Wasannin Na Afcon An Tsara Shi Kamar Haka:
Lahadi, 21 ga Disamba
Rukunin A: Morocco da Comoros, Rabat (19:00)GMT
Litinin, 22 ga Disamba
Rukunin A: Mali da Zambia, Casablanca (14:00)GMT
Rukunin B: Afirka ta Kudu da Angola, Marrakech (17:00)GMT
Rukunin B: Masar da Zimbabwe, Agadir (20:00)GMT
Talata, 23 ga Disamba
Rukunin D: Senegal da Botswana, Tangier (12:30)GMT
Rukuni D: DR Congo da Benin, Rabat (15:00)GMT
Rukunin C: Najeriya da Tanzania, Fes (17:30)GMT
Rukunin C: Tunisia da Uganda, Rabat (20:00)GMT
Laraba, 24 ga Disamba
Rukunin E: Burkina Faso da Equatorial Guinea, Casablanca (12:30)GMT
Rukunin E: Algeria v Sudan, Rabat (15:00)GMT
Rukunin F: Ivory Coast v Mozambique, Marrakech (17:30)GMT
Rukunin F: Kamaru da Gabon, Agadir (20:00)GMT
Juma’a, 26 ga Disamba
Rukunin B: Angola da Zimbabwe, Marrakech (12:30)GMT
Rukunin B: Masar da Afirka ta Kudu, Agadir (15:00)GMT
Rukunin A: Zambia v Comoros, Casablanca (17:30)GMT
Rukunin A: Morocco da Mali, Rabat (20:00)GMT
Asabar, 27 ga Disamba
Rukuni na D: Benin da Botswana, Rabat (12:30)GMT
Rukunin D: Senegal v DR Congo, Tangier (15:00)GMT
Rukunin C: Uganda da Tanzania, Rabat (17:30)GMT
Rukunin C: Najeriya da Tunisia, Fes (20:00)GMT
Lahadi, 28 ga Disamba
Rukunin F: Gabon da Mozambique, Agadir (12:30)GMT
Rukunin E: Equatorial Guinea da Sudan, Casablanca (15:00)GMT
Rukunin E: Algeria da Burkina Faso, Rabat (17:30)GMT
Rukunin F: Ivory Coast da Kamaru, Marrakech (20:00)GMT
Litinin, 29 ga Disamba
Rukunin B: Angola da Masar, Agadir (16:00)GMT
Rukunin B: Zimbabwe da Afirka ta Kudu, Marrakech (16:00)GMT
Rukuni A: Comoros da Mali, Casablanca (19:00)GMT
Rukunin A: Zambia v Morocco, Rabat (19:00)GMT
Talata, 30 ga Disamba
Rukunin C: Tanzania da Tunisia, Rabat (16:00)GMT
Rukunin C: Uganda da Najeriya, Fes (16:00)GMT
Rukunin D: Benin da Senegal, Tangier (19:00)GMT
Rukunin D: Botswana da DR Congo, Rabat (19:00)GMT
Laraba, 31 ga Disamba
Rukunin E: Equatorial Guinea da Algeria, Rabat (16:00)GMT
Rukunin E: Sudan v Burkina Faso, Casablanca (16:00) GMT
Rukunin F: Gabon da Ivory Coast, Marrakech (19:00) GMT
Rukunin F: Mozambique da Kamaru, Agadir (19:00)GMT
Mataki na ƙarshe
Zagaye ƙungiyoyi 16 – Kuma Za’a Fara 3 zuwa 6 Janairu
Asabar, 3 ga Janairu
SR1: Na daya a rukuni D v da na 3 a rukunin B/E/F, a filin Tangier (16:00) GMT
SR2: Wanda ya zo na daya a rukunin A v da na biyu a rukunin C, Casablanca (19:00) GMT
Lahadi, 4 ga Janairu
SR3: Wanda ya zo na daya a rukunin A v da na 3 daga rukunin C/D/E, Rabat (16:00)GMT
SR4: Wanda ya zo na daya a rukunin B v da na biyu a rukunin F, Rabat (19:00)GMT
Litinin, 5 ga Janairu
SR5: Wanda ya zo na daya a rukuni B v da na 3 daga rukunin A/C/D, Agadir (16:00) GMT
SR6: Wanda ya zo na daya a rukuni C v da na 3 a rukunin A/B/F, Fes (19:00) GMT
Talata, 6 ga Janairu
SR7: Wanda ya zo na daya a rukunin E v da na biyu a rukunin D, Rabat (16:00)GMT
SR8: Wanda ya zo na daya a rukuni F da wanda ya zo na biyu a rukunin E, Marrakech (19:00) GMT
Wasan kusa da na kusa da na karshe – Ranar 9 & 10 Janairu
Juma’a, 9 Janairu
QF1: Wanda ya nasara a a wasan SR2 da wanda ya yi nasara a SR1, Tangier (16:00)GMT
QF2: Wanda ya yi nasara a SR4 da wanda ya yi nasara a SR3, Rabat (19:00)GMT
Asabar, 10 ga Janairu
QF3: Wanda ya yi nasara a SR7 da Wanda ya yi nasara a SR6, Marrakech (16:00) GMT
QF4: Wanda ya yi nasara a SR5 da Wanda ya yi nasara a SR8, Agadir (19:00) GMT
Wasan daf da na karshe – 14 ga Janairu
SF1: Wanda ya yi nasara a QF1 da Wanda ya yi nasara a QF4, Tangier (17:00) GMT
SF2: Wanda ya yi nasara a QF3 da Wanda ya yi nasara a QF2, Rabat (20:00) GMT
Wasan neman matsayi na uku – 17 ga Janairu
Casablanca (16:00)GMT
Rabat (19:00)GMT


