Tsohon kyaftin ɗin Super Eagles Ahmed Musa ya sanar da yin ritaya daga ƙwallon ƙafa ta ƙasa da ƙasa, wanda hakan ya kawo ƙarshen shekaru 15 da ya shafe yana wasa wa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Najeriya.
Musa ya sanar da hakan ne a ranar Laraba ta shafin X ɗinsa a hukuma, yana mai bayyana shawarar tasa ta biyo bayan la’akari da ya yi sosai, ya ce sanya rigar kore da fari idan ya tuna abu ne mai ma’ana sosai a gare shi.
Na tuna lokacin da na fara tafiya ta ƙasa da ƙasa a matsayin matashin ɗan wasa, lokacin da aka gayyace ni zuwa ƙungiyoyin ƙasa na ‘yan ƙasa da shekaru 20, da 23 da manyan ƙungiyoyi, ban taba yin jinkirin zuwa Najeriya ba” in ji shi.
Musa ya ya buga wasanni 111 a ƙungiyar Super Eagles, wanda hakan ya sa ya zama ɗan wasa mafi buga wasa a tarihin ƙwallon ƙafa ta ƙasar.
Ya samu nasarar lashe gasar cin kofin ƙasashen Afirka ta 2013 kuma ya ci gaba da zama ɗan wasan da ya fi zura ƙwallo a Najeriya a gasar cin kofin duniya ta FIFA, inda ya zura ƙwallaye masu kyau a kan Argentina a 2014 da Iceland a 2018.
Ya bayyana cimma wasanni 111 a matsayin babban abin farin ciki da girmamawa ne a koyaushe.
Musa ya ƙara da cewa lashe gasar AFCON ta 2013 wani muhimmin abu ne, zaman kyaftin ɗin ƙungiyar ya koya masa darussa masu mahimmanci game da shugabanci, haƙuri da kuma sanya wasu a gaba.
Babban Manaja kuma ɗan wasan ƙungiyar Kano Pillars ya gode wa abokan aikinsa, masu horarwa, da duk ma’aikatan da kuma masu kula da ƙwallon ƙafa saboda goyon bayan da suka ba shi na tsawon shekaru.
Ya kuma nuna matuƙar godiya ga magoya bayan Najeriya na gida da waje saboda alakar da sukayi da shi a tsawon aikinsa.
Ya kammala da cewa ya ba da dukkanin iyawarsa ga Najeriya kuma yana da kwarin gwiwa game da makomar Super Eagles, ya ƙara da cewa dangantakarsa da ƙasar za ta ci gaba.


