Mutane akalla 8 sun mutu a bayan da wata motar tanka ta daukar mai ta yi karo tare da yin bindiga da sanyin safiyar yau jumma’a a Likomba dake kusa da garin Tiko a yankin kudu maso yammacin Kamaru.
Wani jami’in gundumar da abin ya faru mai suna Vioang Mekala, yace direban motar ya kasa shawo kanta a lokacin da burkinsa ya samu matsala a daidai lokacin da yake gangarawa daga kan wani tudu, inda motar tasa ta buge wasu motocin da kuma gine-gine kafin ta yi bindiga ta kama da wuta.
Mekala ya shaidawa ‘yan jarida cewa tankar ta kone kurmus, tare da wasu motocin, yayin da wuta ta lalata gine-gine da yawa.
Har ya zuwa tsakar rana a yau jumma’a, wasu sojojin kasar dake aikin agaji suna kokarin kashe wutar dake ci a wurin, amma masu aikin gaggawar sun ce watakila adadin wadanda suka mutu zai karu.
An samu irin wannan hatsari na tankokin daukar mai a baya a kasar ta Kamaru, wadda ba ta da bututun jigilar mai a saboda haka tilas ana amfani da motocin tanka wajen jigilarsu ko kuma ta jiragen kasa.


