A kasar Australia shekaru 30 da suka wuce da wani dan bindiga ya kashe mutane 35, babu wata wata shugabannin kasar suka kafa dokar mallakar bindiga mafi tsauri a kasashe dake yammacin turai, amma yanzu bayan harin da aka kai kan masu bikin addini yahudawa ya kashe mutane 15, an kasa samun matsaya kan mataki na gaba dangane da mallakar makamai.
Kiran da PM Anthony Albanese yayi na tsaurara dokokin mallakar bindiga yana fuskantar turjiya daga masu ra’ayin rikau da wasu, wanda yake nuna rarrabuwar kawuna idan aka auna da abunda ya faru shekaru 30 da suka wuce.
Tun bayan da aka kai hari ranar lahadi da ta wuce, shugabanni masu ra’ayin rikau, da yahudawa, suna sukar PM Albanese ya gaza daukar matakai na tunkarar matsalar kyamar yahudawa da yake karuwa a kasar, lamarin da yake kalubale ga shugabancinsa.


