Wani madugu a kungiyar ‘yan tawayen kwango M23 da kasar Rwanda tace bata goyon bayan ta kama daruruwan sojojin Burundi a farmaki data kai a gabashin kasar, inda ake ci gaba da gwabza yaki, duk da gargadin da gwamnatin Trump tayi.
A makon jiya ne M23 ta kama garin Uvira dake kusa da kan iyaka da kasar Burundi, kasa da mako daya, bayan da shugabannin kasashen Kwango Da Rwanda suka sanya hanu kan wata yarjejeniyar zaman lafiya a Washington, a taron da shugaban Amurka Donald Trump ya jagoranta.
A ranar Asabar, sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio yace take taken Rwanda a gabashin jamhuriyar Kwango ya sabawa yarjejeniyar da aka kulla a Washington, daga nan yayi alwashin cewa, “za su dauki matakin ganin cewa an mutunta alkawuran da aka yi wa shugaban na Amurka.”
Rwanda ta karyata zargin cewa tana goyon baya kungiyar M23, ta zargi dakarun kasashen kwango da Burundi da sake sabunta fada a yankin.
MDD a wani rahoto data wallafa cikin watan Yuli, tace Rwanda ce take ruwa da tsaki kan harkokin kunigyar ‘yan tawayen M23.


