Jami,an Tsaron Nigeria sun Samu Nasarar kawar da Wasu Manyan Boma Bomai guda Uku da Ake zaton Yan ta’addan Daji ne Suka Binne su a Jihar Neja.
Rahotanni Daga Yankin kauyen Ganaru a gundumar Zugurma ta karamar Hukumar Mashegu na nuna cewa an Binne Boma Bomai ne akan hanyar Zuwa Wani Daji da ake kira Noma Dole,
kawowa yanzu dai babu wani bayani daga Hukumomin Jihar Nejan akan lamarin sannan babu karin haske akan wadanda ake zargi da binne boma-boman.
Jihar Nejan dai na fama da Matsalar yanbindiga Masu Kisan Jama,a Babu gaira Babu Dalili,
Gano Boma Boman dai yazo ne bayan Kwanaki biyu da yin Kisan Gilla ta hanyar yankan Rago ga kimanin Mutane Mutane 40 a karamar Hukumar Borgu Mai iyaka da karamar Hukumar ta Mashegu.


