Shugaban asibitin Al Shifa dake birnin Gaza, Mohammed Abu Selmia, ya shaidawa kamfanin dillacin labarai na Reuters ranar Jumu’a cewa, Palasdinawa 5 ne suka rasa rayukan su a wani hari da Isra’ila ta kai wata makaranta da ke bawa ’yan gudun hijirar yaki mafaka, a unguwar Tuffah dake gabashin Gaza.

Ma’aikatar bada agajin gaggawa ta Palastine, ta fada a wani jawabi cewa yawancin wadanda aka kashe yara ne, da kuma wasu da aka kai asibiti da raunuka.
Ma’aikatar ta ce basu samu damar daukan gawawwakin ba har sai da ofishin daidata al’amuran jin kai na Majalisar Dinkin Duniya OCHA, ya daidaita da ‘yan Isra’ila.
A cewar ma’aikatar lafiya, idan aka hada da wadannan biyar da aka kashe, adadin palasdinawan da Isra’ila ta kashe ya kai 400, tun bayan ayyana dokar tsagaita wuta da ta fara aiki a watan Octoba.


