Gwamnatin jihar Adamawa ta ayyana dokar hana fita na sa’o’i 24 a karamar hukumar Lamurde, sakamakon sake barkewar rikici a yankin.
Wata sanarwa da mai magana da yawun mataimakin gwamnan jihar Hussaini Hammangabdo, ya fitar a ranar Lahadi ta bayyana cewa an dauki matakin ne bayan sake tashin wata takaddama tsakanin al’ummomin yankin da yammacin ranar Lahadi.
A makon da ya gabata, al’ummomin Bachama da Chobo na karamar hukumar Lamurde sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a dakin taro na Banquet Hall da ke fadar Gwamnati a Yola.
Taron ya hadu da Hama Bachama, Homun Daniel Ismaila, manyan jiga igan al’umma, jami’an gwamnati da hukumomin tsaro.
Sanarwar ta kara da cewa: “Tuni an umurci hukumomin tsaro da su dauki matakan gaggawa domin dawo da zaman lafiya da doka a yankin.”
Gwamnati ta kuma yi kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu tare da nuna da hadin kai domin tabbatar da zaman lafiya a yankin.


