Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Najeriya Taja Hankalin ‘Yan Najeriya Mazauna Iran Da Kasashen Larabawa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnan Gombe Yace An Sace Yara 48 A Jihar Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • ‘Yan Bindiga Suna Cigaba Da Kashe Mutane A Garin Gwana Dake Jihar Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

An tura tsohon ministan Ilimin Nijar gidan yari saboda zargin aikata fyade ga wata daliba.
Published: January 8, 2026 at 1:38 PM | By: Mustapha Nasiru Batsari | Updated: January 8, 2026

Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun cafke tsofon ministan ilimi mai zurfi PhD Mamadou Djibo sakamakon zargin yi wa wata daliba fyade. Tuni a ka wuce da shi gidan yari a ci gaba da binciken wannan al’amari da ta farfado da mahawwara game da cin zarafi mata a makarantu.
Wakilin GTA Hausa Amurka ke Magana Souley Moumouni Barma ya aiko mana Karin bayani daga birnin Yamai.
Ainahi tsofon minista Mamodou Djibo ya gurfana a ofishin ‘yan sandan farin kaya inda aka saurare shi bayan da wata daliba ta shigar da kara a bisa zarginsa da yi ma ta fyade. Daga bisani maganar ta kara gaba zuwa kotu inda alkali mai tuhuma ya damka shi a hannun alkali mai bincike wanne ya tura shi gidan yarin Kollo a ci gaba da bincike. abinda ‘yan kasa ke ganin alama ce ta yunkurin zartas da abubuwan da dokokin kasa suka yi tanadi dangane da batun cin zarafin mata. Alhaji Abdou Maman Lokoko na daga cikin shugabanin kungiyoyin bunkasa ilimi a Nijar.

Majiyoyi na cewa dalibar da ta bankado wannan badakala na daga cikin daliban makarantar da ke karatu a makarantar tsofon minista PhD Mamadou Djibo lamarin da ke farfado da mahawwara game da yanayin da dalibai mata ke karatu cikinsa. Wata ‘yar fafutika Housseina Maizoumbou na ganin lokaci ya yi da za a kawo karshen matsalar.

A nan gaba ne a ke saran gurfanar da tsohon ministan na ilimi a gaban alkali domin tantance zahirin abubuwan da suka faru.
Dan rajin kare hakkin dan adam Abdourahamane Oumarou na cewa…

Kawo yanzu ba wani takamemen bayani daga bangaren mashara’anta haka kuma wani makusancin ministan da ke zargi ko laiyansa ba su ce kala ba game da wannan dambarwa.

An tura tsohon ministan Ilimin Nijar gidan yari saboda zargin aikata fyade.

https://gtahausa.com/wp-content/uploads/2026/01/TSOHON-MINISTA-NIJAR.mp3
Afrika

Post navigation

Previous Post: Amurka Ta Kama Tsohon Ministan Kudin Kasar Ghana
Next Post: Sarkin Kagarko Ya Rasu Yana Da Shekaru 110

Karin Labarai Masu Alaka

‘Yan Gudun Hijira A Kasar Libya Suna Fuskantar Cin Zarafi Afrika
Afirka Ta Kudu Ta Bukaci Jakadan Israela Ya Fice Daga Kasar Afrika
ECOWAS Zata Kafa Rundunar Yaki Da Rashin Tsaro Afrika
ECOWAS Ta Saka Dokar Ta Baci A Afrika Ta Yamma Afrika
Kamfanin Jiragen Saman Ethiopia Zai Kafa Babban Filin Jirgi Afrika
Yan Bindiga Suna Cigaba Da Kashe Mutane A Garin Gwana Dake Jihar Bauchi Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ‘Yan Uwa Musulmi A Jihar Gombe Sunyi Allah Wadai Da Kisan Ayatollah Khomeini
  • An Samu Kaburbura Biyu Dauke Da Gawarwaki 173 A Kasar Kwango
  • Yan Bindiga Suna Cigaba Da Kashe Mutane A Garin Gwana Dake Jihar Bauchi
  • Karancin Iskar Gas Kalubale Ne Ga Wutar Lantarki
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Hukumar NAPTIP Ta Kubutar Da Yara 11 Daga Hannun Masu Safara Mutane Labarai
  • An Kama Masu Fasa Kaurin Gawayi A Malawi Afrika
  • Gwamnan Jihar Filato Na Shirin Komawa APC Siyasa
  • Kasar Togo Ta Kori Paul Henri Damiba Zuwa Kasar Sa Ta Haihuwa Afrika
  • Jam’iyar APC A Najeriya Ta Kaddamar Da Bada Shaidar Zama Dan Jam’iyyar Ta Na’ura Mai Kwakwalwa Siyasa
  • An Gurfaranar Da Wadanda Ake Zargi Takai Hari Gaban Kotu Najeriya
  • Gwamnatin Najeriya Da Haɗin Guiwar Gwamnatin Jihar Zamfara Suna Shirin Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Jihar Rumbun Hotuna
  • GTA Hausa Logo
    Shirin Dare 2030 UTC Yau Juma’a 11.21.2025 Rediyo
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.