Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Najeriya Taja Hankalin ‘Yan Najeriya Mazauna Iran Da Kasashen Larabawa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnan Gombe Yace An Sace Yara 48 A Jihar Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • ‘Yan Bindiga Suna Cigaba Da Kashe Mutane A Garin Gwana Dake Jihar Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Jagorancin Wikki Tourist FC Na Samun Yabo
Published: November 25, 2025 at 2:12 PM | By: Bala Hassan | Updated: November 25, 2025

Umar Aliyu, Shugaban Magoya Bayan Wikki Tourist

Tabbas Wikki Tourist ta samu shuwagabanin da zasu cire mata kitse a wuta. Wannan yabo ya fito ne ta bakin Shugaban ƙungiyar Magoya bayan Ƙungiyar kwallon kafa ta Wikki Tourist Fc da ke Bauchi a tarayyar Najeriya. Alh Umar (Aljan) yayi karin hasake a wata ganawa da yayi da wakilin GTA Hausa.

Umar ya ce ƙungiyar ta samu dai dai tuwa a karkashin jagorancin shugaban gudanawar Kulub din Alh. Auwal Gotel, lura da yadda ƙungiyar ta ke samun nasara a wasannin ta a gida da waje ” In ji Aljan.

Yace a baya akwai wasu abubuwa na kurakurai da aka yi bangaren Shuwagabanni sakamakon jan hankali da ake musu ta kafafen yada labari ko mai ya dai dai ta a yanzu.

Har ila yau ‘Aljan, ya yaba wa manbobinsa bangaren magoya baya bisa yadda suke bin doka da oda wajan ganin anyi wasa lafiya, don kuwa ko da za’a zo gida a Wikki Tourist ta yi kunnen doki baza a ta da yamutsi ba, kamar yadda wasu ƙungiyoyin ke yi.

A ranar Lahadi da ta gabata ƙungiyar kwallon kafa ta Bayelsa United ta zo har gida ta rike Wikki 1-1 a wasan mako na 14, cikin gasar Firimiyar Najeriya na bana, amman babu wani abun da ya faru na cin mutuncin alkalin wasa ko wani jami’i, duk da irin kurakuren da baza’a rasa ba daga Alkalin wasa.

Umar yace duk kulub din Arewa da suke buga gasar Firimiyar Najeriya NPFL 2025/26 babu wadda ta kai Wikki Tourist kokari ganin yadda ita ce kawai ba’ayi nasara akanta a gidan ta ba.

Yanzu haka Wikki Tourist FC ta na mataki na 7 a teburen gasar Firimiyar Najeriya mako na 14, a ranar Asabar 29 ga watan Nuwamban 2025, zata kai bakunci zuwa gidan ƙungiyar kwallon kafa ta Bendel Insurance FC, wasannin mako na 15.

Wasanni

Post navigation

Previous Post: Kano Pillars Ta Doke Ikorodu City
Next Post: An Kubutar Da ‘Yan Matan Sakandire Su 24 Na Jihar Kebbi

Karin Labarai Masu Alaka

Da Alamu Ronaldo Zai Buga Dukkan Wasanni Da Gasar Kofin Duniya A 2026 Wasanni
Nasarawa Ce Zakara A Wasan Kwallon Kafa Ta Kurame 2025 Wasanni
Chelle: Rashin Jituwa Tsakanin Osimhen Da Lookman Matsala Ce Ta Cikin Gida Wasanni
Za’a Dauko Messi Aro Zuwa Barcelona Deco Wasanni
FIFA Ta Yi Wa Malaysia Kaca-kaca Wasanni
Manya-Manyan Wasannin Wannan Makon Wasanni

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ‘Yan Uwa Musulmi A Jihar Gombe Sunyi Allah Wadai Da Kisan Ayatollah Khomeini
  • An Samu Kaburbura Biyu Dauke Da Gawarwaki 173 A Kasar Kwango
  • Yan Bindiga Suna Cigaba Da Kashe Mutane A Garin Gwana Dake Jihar Bauchi
  • Karancin Iskar Gas Kalubale Ne Ga Wutar Lantarki
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • CAF Ta Ci Tarar Ƙasar Masar Dala 5,000 AFCON 2025 Wasanni
  • Hukumomin Taliban Sunce A Shirye Suke Domin Sulhu Afrika
  • Majalisar Dattawar Najeriya Ta Amince Da Tura Sakamakon Zabe Ta Intanet Labarai
  • Kasar Sham Ta Sanar Da Tsagaita Wuta Tsakaninta Da Kungiyar Kurdawa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Shugaba Tinubu Ya Gana Da Wasu Gwamnoni Shida Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mace Ta Farko Da Zata Shugabanci Jami’ar Northwest Dake Kano Najeriya
  • Kasashen Thailand Da Cambodia Sun Amince Da Tsagaita Wuta Labarai
  • Kamfanin Jiragen Saman Ethiopia Zai Kafa Babban Filin Jirgi Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.