An yankewa tsohon prime ministan Tunisia Ali Larayedh hukuncin daurin shekaru 24 a gidan yari, kan kama shi da laifin taimakawa masu halin rikau ‘yan Tunisia zuwa kasar Sham a cikin shekaru 10 da suka wuce, a cewar kafar yada labarai ta kasar.
Jam’iyyar sa ta IOE ta ce Wannan bita da kullin siyasa ne, kuma yana daga cikin yunkurin shugaban na dakile ‘yan adawa, biyo bayan mamayar karfin mulkin da shugaba Kais Saied yayi a shekarar 2021 lokacin da ya rushe majalisun kasar.
Larayedh ya rike ragamar prime minister daga shekarar 2013 zuwa 2014, lokacin da kasar ke cikin ya mutsi biyo bayan juyin juya halin da aka yi a 2011.
Larayedh, wanda ke tsare tun 2022, ya fadawa kotu, a ranar Alhamis cewa shi bashi da laifi, kuma an danne masa hakkin sa. Yana da damar da zai daukaka kara kan laifin da aka kama shi da shi da kuma hukuncin da aka yanke masa.


