Al’ummar kasar Kenya suna jimamin mutuwar wani namijin giwa da yayi suna a kasar, mai haure babba, wanda kuma jimawar da yayi a raye ta zamo abar misali da kokarin da kasar ke yi na kare giwaye daga mafarautan dake kashe su don cire musu haure.

Wannan giwa mai suna Craig, wanda ya mutu ranar asabar, ya rayu a wani gandun daji da ake kira Amboseli a kudancin kasar, inda ake daukar matakan kare dabbobin dake cikinsa, kuma yana daya daga cikin wuraren da ‘yan yawon bude ido da shakatawa suka fi ziyarta.
Hukumar kula da namun daji ta kasar Kenya ta bada sanarwa cewa Craig, wanda yayi suna saboda haurensa da kusan ke jan kasa saboda girmansa, ya mutu yana da shekaru 54 a duniya.
Gidan telebijin na NTV na kasar ya watsa shiri na musamman game da mutuwar wannan giwa, yana mai cewa Craig na daya daga cikin manyan giwaye masu gagarumin haure su kalilan da suka rage a nahiyar Afirka.


