Daraktan wasanni na Barcelona, Deco, ya dakatar da tattaunawa game da yiwuwar amfani da damar da MLS ke da ita ta na daukan dan wasan Inter Miami, Lionel Messi a matsayin aro, yana mai cewa hakan ba zai yiwu ba.
Maganar komawar Lionel Messi Turai a matsayin aro na ɗan gajeren lokaci a lokacin hutun kakar wasa ta kasar Amurka MLS (tsakiyar Disamba zuwa tsakiyar Fabrairu) ta samu karbuwa ne bayan da aka ruwaito cewa tsarin sabon kwantiraginsa da Inter Miami ya ba shi damar zuwa wata ƙungiya na wucin gadi don ci gaba da karfafa da kyautata ingancin wasansa kafin gasar cin kofin duniya ta 2026 da za’ayi a kasashen Amurka Mexico da Kanada.

Kungiyoyi da dama, ciki har da Tsohuwar kulub din sa Barcelona, na bukatar sa a matsayin aro a tunanin magoya baya inda suke rera waka da sunan Messi a minti na 10 na kowane wasa tun bayan komawarsu Camp Nou, tare da wasu bangaren ‘yan jarida.
Ita ma ƙungiyar Galatasaray an alakanta su a matsayin masu karban Messi da dan gajeren lokaci a cikin waɗannan rahotannin.
Deco daraktan wasanni na Barcelona, , ya soki wannan ra’ayin.
Da aka tambaye shi game da yiwuwar zuwa aro na hunturu, Deco ya ce “ba zai yiwu ba” kuma ya jaddada cewa Messi “yana da kwangila” da ƙungiyar Inter Miami na ƙasar Amurka.


