A karon farko tun bayan da gwamnatin Nijar ta kudiri aniyar maka kamfanin Orano a kotu, kungiyoyin farar hula a kasar sun jaddada goyon baya kan abin da suka kira yunkurin kwato ‘yancin a kan sha’anin ma’adanai.
Kungiyoyin sun kuma shawarci hukumomin na Nijar da su janye lasisin hakar zinare daga hannun kamfanonin da suka yi kaka-gida don mayar da komai a hannun ‘yan kasa.
A wata sanarwar da ta fitar ne kungiyar M62 ta bayyana matsayinta dangane da kace nacen da ya taso a tsakanin hukumomin Nijar, da kamfanin Orano na Faransa bayan da Nijar ta fara kwashe ton ton na Uranium din da ke jibge shekaru sama da biyu a garin Arlit.
Kungiyar tace ta na goyon matakin da gwamnatin Nijar ta dauka, wanda ta ke ganinsa tamkar matakin kawo karshen mulkin mallakar da aka shafe shekaru fiye da 60 a na yi wa kasar harakar Uranium. Falmata Taya na daga cikin shugabanin M62.
Ita ma kungiyar FRSA mai da’awar kwato ‘yancin kai Afirka a sanarwar da ta bayar ta bayyana gamsuwa da abin da ta kira sabon babin da gwamnatin Abdourahamane Tiani ta bude a fannin ma’adanan karkashin kasa. Salissou Ibrahim shine sakataren watsa labaran kungiyar.
Ko baya ga harakar Uranium kungiyar M62 na ganin bukatar gwamnatin Nijar ta fadada sauye sauyen da ta fara zuwa sha’anin hakar zinare.
Mahawwara kan hurumin fitar da Uranium zuwa waje a tsakanin gwamnatin Nijar da kamfanin Orano na Faransa na ci gaba da karfafa ne a wani lokacin da bangarorin biyu ke jiran hukuncin kotun CIRDI dangane da makomar ton 1300 na Uranium da ke girke a yankin arewacin Nijar.
M62 ta bukaci hukumomin kasar su gudanar da bincike kan illahirin aiyukan bankin duniya saboda alakarsu da kotun CIRDI.


