Attajirin dan kasuwa kuma Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Dakta Aliko Dangote, ya kai ƙara gaban Hukumar ICPC yana neman a binciki Manajan Darakta Hukumar sanya ido kan hada-hadar Albarkatun Man fetur (NMDPRA), Farouk Ahmed, bisa zargin cin hanci da rashawa da rayuwa sama da ƙarfin albashin ma’aikacin gwamnati.
Dangote ya yi zargin cewa Ahmed ya biya sama da dala miliyan 7 a matsayin kuɗin makaranta ga ‘ya’yansa huɗu a makarantu daban-daban a Switzerland, kuɗin da ya ce ba zai yiwu a samo shi daga dukkan albashinsa na aikin gwamnati ba.

A cikin ƙorafin, Dangote ya zargi shugaban NMDPRA da karkatar da kuɗaɗen gwamnati ta hanyar amfani da ofishinsa domin amfanin kansa, lamarin da ya ce ya cutar da ƙasar kuma ya jawo ce-ce-ku-ce a bainar jama’a.
Ya buƙaci ICPC ta binciki zargin tare da kamashi da gurfanar da Ahmed idan aka same shi da laifi, yana mai cewa a shirye yake ya gabatar da hujjoji idan aka gayyace shi.


