Farashin dalar Amurka ya yi sama ranar Jumu’a, abin da ya wanke raunin da ta yi kan yawancin kudade.
Tashin ya biyo bayan faduwar da tayi, da kashi 9 cikin dari, wanda bata taba kai haka ba tun shekarar 2017, a dalilin tsarin kudin ruwa na bashi, da rigingimun kasuwanci na duniya.
Bayanan da zasu zo ne, mako me zuwa, da kuma bayanai kan biyan kudin ma’aikata zai nuna alamar ko babban bankin kasar Zai rage kudin ruwan bashi.


